| Hausa
KIMIYYA DA FASAHA
3 minti karatu
Butum-butumin NASA ya ɗauki yadda aka yi walƙiya a duniyar Mars a lamarin da ba a taɓa gani ba
Masana sun dade suna muhawara kan ko ana iya samun fitar wutar lantarki a cikin yanayin Mars mai ƙura da ba a san shi sosai ba — amma samun shaidar ya kasance mai wuya.
Butum-butumin NASA ya ɗauki yadda aka yi walƙiya a duniyar Mars a lamarin da ba a taɓa gani ba
Butum-butumin NASA ya ɗauki yadda aka yi walƙiya a duniyar Mars a lamarin da ba a taɓa gani ba / Reuters
28 Nuwamba 2025

Wani butum-butumin hukumar binciken kimiyya ta sararin samaniya ta Amurka, NASA ta sami shaidu na farko na yadda aka yi walƙiya a Duniyar Mars, inda makirfo ɗinsa ya ɗauki sautin "rugugin aradun" da yadda ya karaɗe doron duniyar.

Masana sun dade suna muhawara kan ko ana iya samun fitar wutar lantarki a cikin yanayin Mars mai ƙura da ba a san shi sosai ba — amma samun shaidar ya kasance mai wuya.

Yanzu dai ya bayyana cewa mutum-mutumin Perseverance na NASA, wadda ke yawo a jar duniyar tun 2021, yana naɗar duk sautin walƙiya, in ji wani nazari da aka wallafa a Mujallar Nature a wannan makon.

Sai dai wannan walƙiyar ta Mars ba ta yi kama da manyan walƙiyoyi masu ƙara da nisan tafiya ba kamar irin wanda muke gani a Duniyar Earth.

Maimakon haka, su "ƙananan walƙiya ne masu wucewa da gaggawa" kamar "abin da zaka ji a lokacin busasshen yanayi idan ka taɓa ƙofar motarka tare da ɗan tartsatsin wuta," in ji marubucin jagora Baptiste Chide na cibiyar bincike CNRS ta Faransa ga AFP.

Duk da ƙarancin ƙarfin su, wuta tana ɗan tartsatsi "a kowane lokaci — kuma a ko'ina" a Mars, in ji masanin duniyar.

Tsarin yana farawa ne idan ƙananan ƙurar suka haɗu da juna. Sukan sami caji na lantarki kuma su sake wannan caji kaɗan-kadan.

A nan Duniyar Eath, guguwar ƙura da ƙananan madatsun iska na ƙura a yankunan hamada ma suna ƙirƙirar tartsatsin lantarki. Amma waɗannan ba sa yawan taruwa zuwa ga fitowar wutar lantarki.

Amma a Mars, "saboda ƙarancin matsi sosai da kuma haɗin sinadaran sararin samaniya, adadin caji da ake buƙata ya taru kafin a samu fitowar wuta ya fi ƙaranci," in ji Chide.

An dade da yin hasashen wannan lamari tun lokacin da aka fara bincike a Mars — kuma an ma maimaita shi a dakin gwaje-gwaje.

Chide ya ce ya kasance "babban batu ga kimiyyar Mars" har an sanya wata na'ura a kan na'urar saukar Schiaparelli ta Hukumar Sararin Samaniya ta Turai (ESA) domin neman shi.

Abin baƙin ciki, jirgin ya tarwatse yayin ƙoƙarin sauka a Mars a 2016.

Tun daga lokacin, "ya zama wani abu da aka ɗan manta da shi a binciken Mars," in ji Chide.

Daniel Mitchard, ƙwararren mai nazarin walƙiya a Jami'ar Cardiff wanda bai shiga wannan binciken ba, ya yi sharhi a mujallar Nature cewa binciken ya bayar da "shaida mai gamsarwa game da fitowar wuta sakamakon ƙura".

Amma saboda fitowar wutar "an ji su ne kawai ba a gani ba," ya yi tsammanin muhawarar masana kan wannan batu "za ta ci gaba na wani lokaci."

Wannan bincike na iya kawo wasu bayanai kan sirrin yanayin Mars.