Tsohon kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa ya yi ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa.
Shahararren ɗanwasan mai shekaru 33 ya sanar da wannan mataki nasa ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Larabar nan 17 ga Disamban 2025.
A saƙon nasa ya ce, “Bayan dogon tunani, na yanke shawarar yin ritaya daga ƙwallo a matakin ƙasa-da-ƙasa, wanda ya kawo ƙarshen shekara 15 ina buga wa Super Eagles.
“Na saka bajon [tawagar ƙasata] tsawon shekara 15 cike da alfahari. Tun sanda ina shekara 17 na fara amsa duk kiran da aka yi min wanda ya sa na fi kowa buga wa Nijeriya har sau 111.”
Ɗanwasan da aka haifa a birnin Jos na Jihar Filato a Nijeriya, shi ne wanda ya fi kowa cin ƙwallaye wa tawagar Super Eagles a gasar kofin duniya, da ƙwallo huɗu.
“Na ba da duk iyawata… Na gode Nijeriya… zuciyata za ta ci gaba da zama koriya [ya kalar tawagar Nijeriya]”, inji ɗanwasan.
Buga wa tawagogi
Tun yana matashi, Ahmed Musa ya samu kiran shiga tawagar Nijeriya ta ‘yanƙasa da shekara 17, daga nan kuma ya shiga tawagar ‘yanƙasa da shekara 23, kafin daga bisani a kira shi babbar tawagar Super Eagles.
Daga 2010 da ya shiga babbar tawagar da ya ci ƙwallaye 16, kuma ya buga mata har sau 111, wani abu da ya ce yana alfahari da shi a rayuwarsa.
A shekarar 2013, Ahmed na cikin tawagar da ta lashe kofin ƙasashen Afirka na AFCON, tawagar da kuma ya jagoranta a matsayin kyaftin na tsawon lokaci.
Sau biyu ana karrama ɗanwasan da lambar yabo ta MON, da kuma OON, bayan nuna bajinta tare da Super Eagles a lokuta daban-daban.
A yanzu yana buga wa ƙungiyar Kano Pillars ta Jihar Kano a Nijeriya. Kuma ya zama shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar a shekarar ta 2025.




















