KASUWANCI
2 minti karatu
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta makamashi da tattalin arziki
Tallafin, daga Asusun Raya ƙasashen Afirka, zai ba da gudunmawar kashi na farko na shirin Gudanar da Harkokin Makamashi da shirin tallafa wa tattalin arzikin ƙasa.
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta makamashi da tattalin arziki
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta Makamashi da Tattalin Arziki / TRT Afrika Hausa
10 awanni baya

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta samu kusan CFA biliyan 81 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 145 daga Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB) domin inganta fannin makamashinta da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki.

Firaiministan kasar Ali Mahamane Lamine Zeine da shugaban AfDB Sidi Ould Tah ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Abidjan a ranar Laraba.

Tallafin, daga Asusun Raya Afirka, zai ba da gudunmawar kashi na farko na shirin Gudanar da Harkokin Makamashi da shirin tallafa wa tattalin arzikin ƙasa.

Shirin na da nufin fadada hanyoyin samar da wutar lantarki, da inganta harkokin tattalin arziki, da karfafa rawar da kamfanoni masu zaman kansu ke takawa wajen ci gaban Nijar.

A halin yanzu kashi 22.5% na ‘yan Nijar ne ke samun wutar lantarki, kuma Shirin ya ƙuduri aniyya mayar da hankali wajen samar kashi 30% nan da shekarar 2026, tare da samar da megawatt 50 na makamashin hasken rana a shekarar, sai kuma megawatt 240 nan da shekarar 2030.

Firaiminista Ali Mahamane Lamine Zeine ya ce sauye-sauyen za su haifar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta yanayin rayuwa, yayin da shugaban bankin AfDB, Sidi Ould Tah ya jaddada ci gaba da goyon bayan bankin na dogon lokaci.

Baya ga makamashi, yarjejeniyar ta hada da matakan bunƙasa kudaɗen haraji, da biyan basussukan cikin gida, da kuma bunƙasa ci-gaban kamfanoni masu zaman kansu.

Wannan yunƙurin dai wani babban mataki ne a ƙoƙarin da gwamnatin Nijar ke yi na samar da ci gaba mai ma'ana da kuma 'yanci na makamashi.