Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun yi nasarar tarwatsa wani shirin kai hari da dare kan al’ummomin Chibok a Jihar Borno.
Harin, wanda fiye da ’yan ta’adda 300 suka ƙaddamar daga wurare da dama, ya fara ne kimanin ƙarfe 02:00 na asuba a ranar Asabar, amma an fatattake su gaba ɗaya ta hanyar samun bayanan sirri da kuma dubarun yaƙi da amfani da makamai masu ƙarfi inda dakarun runduna ta 28 ta Task Force Brigade ne suka yi wannan aiki.
A cewar wata sanarwa daga rundunar, sojojin ke cikin shirin ko-ta-kwana ne suka ga alamun motsin abokan gaba, wanda hakan ya ba su dama cikin gaggawa suka shirya yaƙi da ‘yan ta’addan daga fagagen daga daban-daban. Sun yi musayar wuta ta fiye da awa biyu inda jaruman sojojin suka tsaya tsayin daka suka kuma hana ’yan ta’addan kutsawa cikin garuruwan da ke makwabtaka.
Bayan ‘yan ta’addan sun ga alamar asubahi ta yi, sai suka fara janyewa zuwa hanyar Azir ta cikin dajin Sambisa, inda suka yi yunƙurin tsallakawa ta hanyar Damboa zuwa Biu.
Sakamakon haka, sai aka bayar da umarni ga Brigade ta 28 da su yi kwanton-ɓauna kafin gadar Azir domin hana ‘yan ta’addan tserewa da kuma halaka su, inda jirgi maras matuƙi na sojojin Nijeriya ya taimaka musu da hakan.
A sanarwar da sojojin suka fitar, sun ce sojojin sama na Operation Hadin Kai sun aika da jirgin yaƙin Super Tucano domin taimakawa wurin fatattakar ‘yan ta’addan.
Sojojin sun ce babu wani soja da ya rasa ransa kuma babu makamin da ya ɓace a yayin wannan aikin.
Jihar Borno na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ke fama da rashin tsaro musamman rikicin ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.
Duk da a kwanakin baya an samu sauƙin hare-haren ‘yan ta’addan amma a baya-bayan nan sun dawo da kai hare-hare inda ko a watan nan na Nuwamba sai da suka kashe wani sojan ƙasar mai muƙamin Birgediya Janar.












