Yadda birai suka addabi wani gari a Afirka ta Kudu da "sata da ƙwace"
An yi ta yaɗa bidiyoyin yadda biran suke wadaƙarsu a garin.
Yadda birai suka addabi wani gari a Afirka ta Kudu da "sata da ƙwace"
Hukumomin suna nuna damuwa a kan yadda waɗannan birai suka daina jin tsoro ko shakkar mutane kwata-kwata.
25 Yuli 2025

A cikin ƙauyen Simon’s Town da ke kusa da teku a ƙasar Afirka ta Kudu, inda gaɓar Tekun Atlantika take kusa da Gandun Dajina Table Mountain, wani al'amari mai ban mamaki yana faruwa.

Birai sun gallabi yankin, irin birran da aka fi sani da Cape baboons, sai dai mutanen wajen ba sa jin daɗin hakan sam.

A garin Simon's Town, maimakon birai su yi ta tsalle-tsallensu na da aka san su da shi daga wannan bishiya zuwa waccar, sai su yi ta dirga a saman rufin gidajen mutane suna cire rufin kwano.

Bidiyoyi sun yaɗu sosai a kafofin sada zumunta, waɗanda ke nuna yadda birrai ke shiga shaguna, suna kwashe 'ya'yan itatuwa sai su gudu.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata, mazauna garin sun fusata inda suka bazama kan titi don yin zanga-zanga, suna neman gwamnati ta dauki matakin gaggawa.

Masu zanga-zangar sun bukaci a aiwatar da tsarin kula da shara mai inganci da kuma sanya tara ga mazauna da masu yawon bude ido da ke ciyar da birai, wanda hakan ke ƙarfafa su su zauna kusa da mutane.

Hukumomi sun nuna damuwa cewa wasu daga cikin waɗannan birrai ba sa jin tsoron mutane, suna nuna halayen tashin hankali da ke haifar da damuwa ga tsaron mazauna.

A garin Kommetjie da ke kusa, kimanin kilomita 45 daga Cape Town, masu fafutuka sun ce ƙarin gidaje da ake ginawa na rage wuraren zama na birai, wanda ke ƙara yawan rikici tsakanin mutane da birai.

Hukumar birnin Cape Town ta bayyana cewa tana fama da ƙalubalen shawo kan kimanin birrai 500 na chacma da ke yawo a Cape Peninsula.

A shekarar 2022, Ma’aikatar Gandun Daji tare da ofishin Magajin Garin Cape Town sun kafa wata tawagar haɗin gwiwa don ƙirƙirar shiri mai ɗorewa na kula da yawan birrai na chacma a Cape Peninsula.

Masu zanga-zangar ba su gamsu da aikin tawagar ba, sun kuma bukaci hukumomi su koma kan muhimman shawarwarin Tsarin Gudanar da Birrai na 2023, wanda ya haɗa da kula da shara da sanya shinge, da aiwatar da dokoki.

Masu zanga-zangar sun kuma nuna adawa da amfani da dabarun kashe birrai, ciki har da tilasta musu barin wuraren ko kashe su.

Kungiyar Kasa da Kasa ta Kula da Kiwon Dabbobi (IUCN) ta ce yayin da yawan mutane ke ƙaruwa, gine-ginen birane da ci gaban noma suna ci gaba da mamaye wuraren zama na birrai na chacma.

An ruwaito cewa birrai 33 sun mutu tsakanin Yuli 2023 zuwa Yuni 2024 sakamakon rikici tsakanin mutane da birrai.

A shekarar 2021, birnin ya kashe wani babban biri wanda ya yi fice wajen shiga gidajen mutane fiye da sau 40 don neman abinci a cikin kwandon shara da farfajiyoyi, har ma yana shiga gidaje yayin da mutane ke ciki.

Rumbun Labarai
Yadda ɗaliban Nijeriya suka samu zantawa da ‘yar-sama-jannati da ke Tashar ISS a sararin samaniya
Yadda dafa abinci na haɗin gwiwa a Somaliya ke ciyar da ɗaruruwan Falasɗinawa a Gaza
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
Sabon nazarin WHO da ke shawartar a daina dukan yara da nufin gyaran tarbiyyarsu
Yadda ƙasaitaccen bikin 'yar hamshakin attajirin Nijeriya Femi Otedola, Temi ya ɗau hankali
Hotunan yadda dubban Musulmai a ƙasashen duniya suka yi murnar Maulidin Annabi
Ranar Hausa ta Duniya ta 2025 ta ƙayatar da gagarumin biki a Daura
Manufar bai ɗaya ta tsare harshe ta hade kawunan al’ummar Songhay-Zarma-Dendi
Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi bayan ya gabatar da shirye-shiryen rediyo mafi tsawo a tarihi
Amaren Gaza: Matan da yaƙin Isra’ila ya mayar zawarawa rabi da rabi
Yadda bikin Rahama Sadau ya zo da mamaki amma ya samu yabo
Hotunan yadda ake tashin talakawa masu kwana a titi a birnin Washington na Amurka
Hijirar tsuntsaye: Afrika na tattaro kan duniya wajen ceto muhimman fadamu don biliyoyin tsuntsaye
Tsutsar Mopane: Daddaɗan abincin Namibia da ake ci tsawon zamanai
Maryam Bukar Alhanislam: 'Yar Nijeriyar da ta zama jakadiyar zaman lafiyar MDD ta farko a duniya
Dalilan da suka sa ake buƙatar mutane su samu abokai na zahiri a yayin da intanet ke jawo kaɗaitaka
Nairobi Birdman: Matashin da ke abota da tsuntsaye a Kenya
Abin da ya sa Kabul zai iya zama babban birni na farko da zai fuskanci matsalar rashin ruwa a duniya
Bikin Wasannin Al’adu Karo na 7 ya farfado da hadin kan al’adu, iyalai da ma duniya
Waiwaye kan tarihin Aikin Hajjin Annabta da yadda ake gudanar da shi