| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Jihar Borno ta karɓi 'yan gudun hijirar Nijeriya 300 da suka dawo gida daga Kamaru
‘Yan gudun hijirar da suka dawo sun isa garin Pulka ta wata tsararriyar hanya da aka bi, wanda ke nuna wani gagarumin ci gaba da aka samu a ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake dawo da 'yan-gudun-hijira gida na tsawon lokaci.
Gwamnatin Jihar Borno ta karɓi 'yan gudun hijirar Nijeriya 300 da suka dawo gida daga Kamaru
Gwamnatin Jihar Borno ta karbi 'Yangudun hijirar Nijeriya 300 da suka dawo gida / TRT Afrika Hausa
28 Janairu 2026

Gwamnatin Jihar Borno ta shiga mataki na huɗu na shirin mayar da 'yan-gudun-hijira gida inda aka yi nasarar dawo da 'yan-gudun-hijirar Nijeriya 300 zuwa yankin karamar hukumar Gwoza daga ƙasar Kamaru.

‘Yan-gudun-hijirar da suka dawo sun isa garin Pulka ta wata tsararriyar hanya da aka bi, wanda ke nuna wani gagarumin ci gaba da aka samu a ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake dawo da 'yan gudun hijira gida na tsawon lokaci.

Ga iyalai da dama, komawa gida na nuna wani yanayi na farin ciki da godiya da kuma sake gina rayuwarsu bayan shafe fiye da shekaru goma na ƙaura.

Yawancin waɗanda suka dawo sun shafe sama da shekaru 11 a sansanin 'yan gudun hijira na (IDP) da ke Kamaru.

Ci gaban ya biyo bayan ziyarar da Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai sansanin 'yan-gudun-hijira da ke Kamaru a ranar 8 ga Disamba 2025, inda ya sake jaddada alƙawarin gwamnatinsa na tabbatar da cewa duk waɗanda suke saon dawowa bisa raddin kansu.

Shugaban Kwamitin mayar da ‘yan gudun hijirar jihar Borno gida, Lawan Abba Wakilbe, ya bayyana aikin a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin yanzu ta samu, inda ya ce shirin bai tsaya ga sake maido da ‘yangudun hijirar ba har da sama musu rayuwa mai kyau da sabunta bege a cikin al'ummomin da abin ya shafa.

A yayin da yake nuni kan haɗin gwiwar da aka samu a yankin, Gwamnan Yankin Arewa Mai Nisa na ƙasar Kamaru, Minjinyawa Bakari, “da kansa ya yi wa 'yan gudunhijirar rakiya,” inda “ya sake jaddada kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Kamaru wajen tasirin ayyukan jinƙai da kuma yaki da ta'addanci a Tafkin Chadi.

Kazalika bayan isowar ‘yangudun hijirar Pulka, hukumomin yankin da hukumomin tsaro sun karɓe su hannu biyu, in ji shi.

Kazalika ya kara da cewa, an kuma bai wa kowane magidanci Naira 500,000, yayin da kowace mata aka ba ta N50,000.

Gwamnatin Jihar Borno ta kuma samar da katifu da tiramen zannuwa ga matan, yayin da Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Ƙasa ta rarraba kayan abinci ciki har da shinkafa, gero, wake, da man girki.

Jami'ai sun bayyana cewa wannan matakin wani bangare ne na dabarun sake farfado da al'ummomin da a baya suka rasa matsuguninsu, tare da sake gina wa da kuma maido da muhimman ababen more rayuwa a yankunan da ayyukan 'yan tawaye suka ɗaiɗaita a fadin jihar.