Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta amince da wani gagarumin gyare-gyare da ya ƙuduri aniyar rage tsadar tafiye-tafiyen jiragen sama a tsakanin ƙasashen yankin.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, ƙungiyar ECOWAS ta ce a taron da ta gudanar na watan Disamban 2024 a Abuja, shugabannin ƙasashen yankin da kuma Gwamnatoci sun amince da tsarin cire haraji kan sufurin jiragen sama.
Sannan za kuma a rage cajin kuɗaɗen da ake ƙarba na fasinjoji da tsaro da kashi 25 cikin 100, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairun 2026.
ECOWAS ta ce matakin ya biyo bayan shafe tsawon shekaru ana fuskantar rashin ci gaba a fannin sufurin jiragen sama na Yammacin Afirka, wanda galibi haraji da cajin kuɗaɗe masu yawa suka haifar.
Ta ce hakan ya danne buƙatar tafiye-tafiye da kuma raunata jarin da ake saka wa a fannin kayayyakin more rayuwa na filayen jiragen sama.
Ɗaya daga cikin yankuna mafi tsada zuwa
Binciken da ECOWAS da ƙungiyar Tarayyar Afirka da ƙungiyar Jiragen Sama ta Afirka (AFRAA) da kuma Kungiyar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA) suka gudanar, ya nuna cewa Yammacin Afirka ya kasance daya daga cikin yankuna mafi tsada da ake zuwa ta jiragen sama.
A wasu lokutan fasinjoji kan biya ƙudaden caji daban-daban har sau 66, yayin da a ɓangare guda kamfanonin jiragen sama ke biyan caji daban-daban har sau 100.
ECOWAS ta yi gargaɗin cewa hauhawar farashin kuɗaɗen sufuri na jiragen sama na hana zirga-zirgar fasinjoji, da jinkirin masu zuwa yawon bude ido, tare da kawo cikas ga hanyoyin kasuwanci da taƙaita 'yancin zirga-zirga da kuma haɗewar yankuna.
Hanyoyin shawo kan ƙalubalen
A cewar sanarwar ƙungiyar, an amince da dokar ta wucin gadi kan cajin da ake karɓa da haraji da kuma sauran kuɗaɗe na sufurin jiragen sama ne don magance ƙalubalen tsarin da kuma daidaita sufurin yankin da ka’idojin jiragen sama na duniya.
Kungiyar ta ce ana sa ran matakin zai rage farashin kuɗaɗen tikiti da ƙara yawan fasinjoji, da kuma ƙarfafa kamfanonin jiragen sama na yankin, tare da bunƙasa ayyukan filayen jirgin sama da kuma samar da ƙarin damarmaki na tattalin arziki ga al'ummomin da ke karɓar baƙi.
An umarci ƙasashe mambobin ƙungiyar da su gyara dokoki da tsare-tsarensu don tabbatar da an aiwatar da wannan mataki baƙi ɗaya, yayin da ake sa rana kamfanonin jiragen sama za su rage farashin tikitinsu kai tsaye ga fasinjoji.
ECOWAS ta ƙara da cewa za ta sa ido kan bin wannan doka ta sabuwar hanyar kula da tattalin arzikin sufurin jiragen sama ta yanki da kuma shirye-shiryen tallafa wa cibiyoyin kula da jiragen sama na haɗin gwiwa da kuma daidaiton ƙa'idojin tsaron jiragen sama.
Ƙungiyar ta ce, gyare-gyaren za su iya rage farashin tikitin jiragen sama da kaso 40 cikin 100, kana za su zurfafa haɗin kan yankin da kuma sanya zirga-zirgar jiragen sama ta zama mai araha ga iyalai da 'yankasuwa da al'ummomi a faɗin Yammacin Afirka.











