Marar ganin da ta bude Islamiyya cikin gidansu don koyar da yara
Wata matashiya mai lalurar rashin gani a Jihar Katsinan Nijeriya, Rabi'atu Nasir wacce take koya wa yara karatun Kur'ani a unguwarsu, ta ce ba za ta bari lalurarta ta hana ta neman ilimi da taimaka wa mutane ba.
2 awanni baya
A hirarta da TRT Afrika, Malama Rabi'atu wacce budurwa ce ba ta taɓ aure ba, ta ce tuni ta yi haddar Ƙur'ani kuma tun kafin ta shiga Islamiyya ta fara koyon karatu ta hanyar bin ƙira'ar Sheikh Minshawi, sannan a fannin boko ma ta kai matakin NCE.