14 awanni baya
Hamshaƙin attajirin Nijeriya da ya fi kowa kuɗi a Afrika, Aliko Dangote ya ce tuni yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran ya fara jawo wa mutane da gwamnatoci matsaloli da wahalhalu, kuma ƙasashe irin na Afrika da dama suke fama da basussuka za su ƙara shiga matsala a sakamakon hakan. Dangote ya ce idan har a a daƙile yaƙin ba, to zai iya sa wa a fara aiki daga gida kamar yadda ya faru a lokacin annobar cutar Covid 19.
