12 Satumba 2025
Hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ta fitar da bidiyon CCTV ranar Jumma'a da ke nuna yadda ɗan bindigar da ya harbe Charlie Kirk ya tsere bayan ya kashe shi ranar 10 ga watan Satumba. Charlie dai wani fitaccen mai goyon bayan shugaban Amurka Donald Trump ne, kuma yana goyon bayan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.