Wagner runduna ce mai zaman kanta ta sojojin  haya da dan kasar Rasha Yevgeny Prigozhin ya kafa. /Hoto: Reuters

Boren da kungiyar sojojin hayar Wagner ta Rasha ta yi a makon jiya ya sanya ayar tambaya kan makomar ayyukan kungiyar a nahiyar Afirka.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, ayyukan Wagner na ci gaba da gudana a kasashen Libiya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mali da kuma Sudan.

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya ce Wagner za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a wadannan kasashe duk da sabanin da jagoran sojin haya Yevgeny Prigozhin ya samu da shugabancin rundunar sojin Rasha.

"Daruruwan ma'aikata na Wagner ne ke aiki a matsayin masu ba da horo a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya - babu shakka, za su ci gaba da wannan aikin... Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mali sun bukaci sojojin (kwangila masu zaman kansu) na Wagner su ba su tabbaci kan tsaro a shugabancinsu, a cewar Lavrov a hirar da TRT ta yi da shi.

Libiya

Kungiyar Wagner ta shiga Libiya ne a 2019 don taimaka wa Khalifa Haftar wajen kai hare-hare a birnin Tripoli a wani mataki na fatattakar gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen duniya.

Masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya sun fitar da alkaluma a shekarar 2020 cewa Wagner ta jibge mayakanta kusan 1,200 a Libiya kuma rundunar sojin Amurka a Afirka ta ce jiragen yakin Rasha na kai wa mayakan Wagner karin makamai.

Reuters ya fitar da rahoton cewa, Wagner ta yi amfani da na'urorin kariya ta sama da jiragen yaki daga sansanin sojojin sama na Jufra da ke kudancin birnin Tripoli.

Ana kuma zargin Wagner da kawo mayaka da sojojin haya daga wasu kasashen Afirka da wasu wurare.

Ko da yake an kawo karshen hare-haren da Haftar ya rika kai wa wadanda ba su yi nasara bayan an tsagaita wuta a 2020, Wagner ta ci gaba da ayyukanta a Libiya a Jufra da sauran sansanonin jiragen sama a yankin kudu da gabas, inda masu binciken suka ce tana amfani da wajen ne a matsayin hanyar shiga wasu yankunan Afirka, a cewar Reuters.

Kazalika kungiyar ta bazu a kusa da manyan wuraren da ake hako mai kuma masu bincike sun ce tana da sha’awar kasuwanci da suka hada da samar da makamashi da hanyoyin sadarwar a Libiya.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Sojojin hayar Wagner sun je Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai arzikin ma'adanai a 2018 inda suka taya gwamnati murkushe yakin basasar da ya barke tun shekarar 2012.

Jakadan Rasha a kasar ya fada a wata hira da kamfanin dillancin labaran kasar Rasha RIA a watan Fabrairu cewa "masu horarwa na Rasha" 1,890 ne a kasar.

Manazarta sun ce Wagner ta samu dama ta sarrafa ma'adanan zinare a kasar.

A makon nan ne Amurka ta kakaba takunkumi kan wani kamfanin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wanda ta ce yana da hannu wajen bai wa Wagner kudade ta hanyar mu'amalar zinare ta haramtacciyar hanya.

Mali

Kasashen Rasha da Mali sun ce mayakan Rasha da ke Mali ba sojojin haya ba ne, amma masu horar da sojoji ne da ke taimaka wa dakarun sojin kasar wajen yakar masu tayar da kayar baya da aka kwashe tsawon shekaru ana fafatawa da su da “mayaka masu kaifin kishin Musulunci.”

Shugabannin kasar Mali sun kwace mulki a shekarar 2021 kuma su gayyaci Wagner ne bayan sun nemi tawagar sojojin Faransa da ta fice daga kasar.

A wani rahoto da Reuters ta fitar a 2021 ta ce gwamnati na ba da kwangila kai-tsaye ga Wagner, inda take biyan ta kusan dala miliyan 10.8 a wata.

An zargi mayakan Wagner da hannu a harin da aka kai yankin Moura da ke tsakiyar kasar Mali a bara, inda ake zargin sojojin yankin da wasu da aka zargi mayakan Rasha da kashe daruruwan fararen-hula.

Sudan

Kasashen Yammacin Duniya da jami'an diflomasiyya sun ce Wagner na da hannu a hakar zinare da kuma yada labaran karya da tsare-tsaren murkushe zanga-zanga a Sudan.

Yayin da Moscow ke da alaka da bangarorin rundunar soji biyu wadanda ke rikici da juna a Sudan tun ranar 15 ga Afrilu, ana zargin cewa Wagner na da kyakkyawar alaka da rundunar Rapid Support Forces (RSF).

Wagner ta musanta gudanar da ayyukanta a Sudan, tana mai cewa ma'aikatanta ba su je can ba sama da shekara biyu kenan, kuma ta ce ba ta da hannu a cikin fadan.

A watan Mayu ne Amurka ta zargi Wagner da samar wa RSF makamai masu linzami, "tana ba da gudunmawa ga tsawaita rikicin da ke haifar da karin rudani a yankin".

TRT Afrika da abokan hulda