Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sha alwashin cewa ba za a tilasta wa kasarsa ta goyi bayan kowace kasa ba daga cikin kasashen Yammacin duniya.
Mista Ramaphosa ya bayyana haka ne a lokacin da yake shirin karbar baki domin gudanar da taron kasashe masu tasowa.
Taron wanda za a yi shi a Johannesburg a wannan makon na kasashen BRICS – wadanda suka hada da Brazil da Rasha da India da China da Afirka ta Kudu – zai nemi kara fadada karfin ikon kasashen da kuma sauya tafiyarsu a siyasar duniya.
“Duk da wasu da ke caccakarmu sun fi son su nuna goyon bayansu a bayyane sakamakon bukatunsu na siyasa da ra’ayi, ba za a jawo mu cikin siyasar kasashen Yamma ba,” kamar yadda Ramaphosa ya bayyana a wani jawabi da ya yi wa kasar a ranar Lahadi.
“Mun ki yarda a matsa mana lamba domin mu danganta kanmu da duk wata kasa ta Yamma ko kuma kungiyar kasashen duniya masu karfi,” in ji shi.
Shugaban China Xi Jinping da Firaiministan Indiya Narendra Modi da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva duk za su halarci taron na kasashen BRICS.
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ne zai wakilci kasarsa a taron yayin da Shugaba Vladimir Putin zai shiga taron ta intanet.
Putin ya yanke shawara kan ba zai halarci taron ba sakamakon Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya na nemansa ruwa a jallo.
Wasu daga cikin shugabannin duniya wadanda ba su cikin kungiyar ta BRICS – daga cikinsu har da Ebrahim Raisi na Iran da Shugaban Indoneisa Joko Widodo - - sun tabbatar da za su halarci taron.
Kasashen BRICS su ne ke da daya bisa hudu na tattalin arzikin duniya kuma masu son shiga kungiyar sun karu.
Akalla kasashe 40 sun nuna sha’awarsu ta shiga kungiyar, inda uku daga cikinsu suka aika da takardar bukatarsu.
Afirka ta Kudu ta bukaci a kara fadada kungiyar ta hanyar bayar da dama a shiga.