Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya ce wa'adin mulkinsa zai ƙare ranar 2 ga watan Afrilu kamar yadda dokoki suna tanada, amma bai bayyana ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasar

Wani taro kan mafitar siyasar Senegal da Shugaba Macky Sall ya haɗa ranar Talata ya nemi shugaban ya ci gaba da mulki idan wa'adinsa ya ƙare ranar 2 ga watan Afrilu har sai an zaɓi mutumin da zai maye gurbinsa, kamar yadda shida daga cikin mahalarta taron suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Mahalarta taron "haɗa kan ƙasa" sun "amince" a ɗauki wannan mataki, duk kuwa da adawar da ƴan jam'iyyun hamayya da ƙungiyoyin fararen-hula suka nuna game da shi.

Ranar 3 ga watan Fabrairu ne Shugaba Sall ya ɗage zaɓen shugaban ƙasar wanda aka tsara gudanarwa ranar 25 ga watan da muke ciki.

Ya ce ya ɗauki matakin ne saboda taƙaddama kan jerin sunayen ƴan takara - matakin da jam'iyyun adawa suka yi watsi da shi domin kuwa an amince da aƙalla ƴan takara 19 su tsaya zaɓe.

Matakin ya haddasa zanga-zanga a cikin ƙasar lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum uku sannan yana shan suka daga ƙasashen duniya waɗanda suka ce hakan yunƙurin juyin mulki ne.

Daga bisani Kotun Tsarin Mulkin Senegal ta yi watsi da matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na ɗage zaɓen tana mai cewa hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.

A wani jawabi da Shugaba Sall ya gabatar bayan hukincin kotun, ya ce zai gudanar da zaɓen ƙasar "nan ba da jimawa ba".

Sai dai ya ƙara da cewa: "Amma game da ranar gudanar da zaɓen, za mu ga yadda za ta kaya a yayin da za a yi taron sulhu. Za a iya gudanar da zaɓen kafin ko bayan ranar 2 ga watan Afrilu."

TRT Afrika da abokan hulda