Hukumar zaben ta bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin cewa ta janye daga daukaka karar.,/Hoto:Reuters

Hedikwatar Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya ta ce ba da yawunta wani jami’inta na Kano ya janye karar da ta daukaka game da zaben gwamnan jihar ba.

Wata sanarwa da Kwamishinan hukumar na kasa kuma shugaban sashen wayar da kan jama’a da masu zabe Sam Olumekun ya fitar ranar Asabar ta ce hukumar tana nan daram a kan karar da ta daukaka bayan kotun sauraren kararrakin zabe ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan Kano.

INEC ta kara da cewa an jawo hankalinta game da wasu rahotanni da ke cewa jami’inta da ke kula da harkokin shari’a na Kano ya rubuta wasikar janye karar da ta daukaka bayan kotu ta soke zaben Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, tana mai cewa ba ta umarce shi ya dauki matakin ba.

“Muna so mu bayyana karara cewa ba mu umarci a rubuta wasikar ba. An janye ta kuma an gargadi wannan jami’i,” in ji INEC.

Hukumar zaben ta bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin da ke cewa ta janye daga daukaka karar.

“Muna so mu fada a fili cewa duk karar da aka sanya INEC a cikinta, ya zama wajibi hukumar ta saurare ta. Don haka mun umarci lauyoyinmu su ci gaba da (wannan shari’a) kamar yadda dokar hukumar ta tanada,” a cewar INEC.

Tun da farko wasu rahotanni da aka rika watsawa a soshiyal midiya sun ce INEC ta janye daga daukaka karar, lamarin da ya jawo zazzafar muhawara tsakanin ‘yan APC da NNPP da ma wasu jama’a na jihar ta Kano.

TRT Afrika