Iyalai da ke rayuwa a wani dakin kasa a kusa da filin shakatawa na Kahuzi-Biega./ Hoto: Reuters

Daga Kudra Maliro

Kusan jama'a 10,000 na Batwa da ke Kivu ta Kudu ne suka rasa matsugunansu, bayan an mayar da yankin da suke na adana tsirrai yayin da mahukunta suka yi alkawarin biyan su kudaden fansa.

A 2019, ma'aikatar muhalli da gwamnatin yankin sun amince su bai wa yankin Batwa na Kahuzi-Biega kudin fansar da suka jima suna sauraro, sannan a ba su kasar noma da gina musu asibitoci da makarantu.

Bayan an gaza cika musu wadannan alkawura, jama'ar Batwa da asalinsu mafarauta ne na barazanar dawowa dajin don ci gaba da rayuwa. Tuni wajen ya zama cibiyar kiwon birrai.

Jama'ar sun rayu a wannan waje kafin a kirkiri Filin Shakatawa na Kahuzi-Biega a shekarun 1970.

Akalla Goggon biri 250 da ke Gabashin Lowland na zaune a Filin Kahuzi-Biega./ Hoto: Reuters

Gwamnan Kivi ta Kudu, Theo Ngwabidje Kasi, ya ce suna yin kokarin ganin jama'ar ba su koma dajin ba.

Ya kuma bayyana cewa mahukuntan yankin ba su da isassun kudaden da za su magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da suka addabe su.

Jean-Marie Kasula, shugaban jama'ar pygmy a yankin Muyange ya ce suna mamakin yadda har yanzu gwamnati ta gaza biyan wadannan kudade na fansa kamar yadda ta yi alkawari a 2019, kuma a yanzu kauyukan da jama'ar Batwa ke zaune ba su da kayan more rayuwa.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "na damu sosai yadda na ke ganin yunwa na kashe mutanenmu, kuma babu wata hanya ta doka da za su nemi hakkinsu."

Kayan tarihi da UNESCO ta martaba

Cibiyar kare gandun daji ta 'Institut Congolais pour la Conservation de la Nature (ICCN)' ce ke da alhakin kula da wannan yanki da aka adana tsirrai da dabbobi.

Kokarin TRT Afirka na jin ta bakin cibiyar game da korafe-korafen 'yan kabilar Batwa bai yi nasara ba.

Amma mahukuntan gundumar sun bayyana cewa suna duba bukatar jama'ar.

Kwamishinan yankin Kivu ta Kudu Jeremie Zirumana ya shaida wa TRT Afirka cewa "Muna bincike kan batun takaddamar kasa tsakanin jama'ar Batwa da kungiyar adana gandun daji da dabbobi, kuma za a bayyana wa duniya rahoton."

Al'ummar Batwa ba su da ababenn more rayuwa irin su asibiti, makarantu da sauransu. Hoto: Reuters

Zirumana ya tunatar a cewa "A yanzu haka dai Institut Congolais pour la Conservation de la Nature (ICCN) ke kula da Filin Shakatawa na Kahuzi-Biege, wanda UNESCO ta ayyana a matsayin wajen tarihi na duniya."

Tsare dabbobi

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a 2009 ya bayyana cewa sama da kashi 90 na jama'ar Batwa su 87,000 da ke Kongo sun rasa matsugunansu, wanda gwamnati ta kwace don killace dabbobi.

Filin Shakatawa na Kasa na da dazuzzuka da suke da manyan duwatsu masu aman wuta na Kahuzi da Biega, kuma waje ne da ke dauke da namun dawa.

Daya daga cikin jinsin goggon birrai na Gabashin Lowlan na dab da karewa inda ba su fi guda 250 ba a yanzu kuma suna rayuwa a dajin.

Yankin na jan hankalin 'yan yawon bude ido daga wasu kasashen waje da cikin gida. A lokacin da jama'ar Batwa ke gwagwarmayar karbar hakkinsu, masu kare dabbobi da tsirrai na cewa kiyaye wajen na da muhimmanci.

'Yan kabilar Batwa sun yi amanna cewa hanya mafi adalci ita ce a biya su hakkokinsu na kudaden fansa don su sake gina gidajensu.

TRT Afrika