Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na karbar bakuncin shugabannin kasashen na BRICS. Hoto/South African Presidency

Shugabannin kungiyar kasashe biyar masu tasowa ta BRICS suna yin taro a Afirka ta Kudu yayin da kungiyar ke neman tabbatar da muryarta a matsayin wani mataki na rage mamayen kasashen Yamma a harkokin duniya.

Kasashen na BRICS wadanda suka hada da – Brazil da Rasha da Indiya da China da Afirka ta Kudu – su ke da kashi daya bisa hudu na tattalin arzikin duniya, haka kuma bukatar shiga kungiyar ta yi matukar karuwa gabannin taron kungiyar na kwanaki uku a Johannesburg.

An kara tsaurara tsaro a birnin inda Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya karbi bakuncin Shugaba Xi Jinping na China da Firaiministan Indiya Narendra Modi da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da kuma wasu shugabannin Afirka 50.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ke nema ta kama shi kan zargin laifukan yaki a Ukraine, ba zai halarci taron ba sai dai ya wakilta ministan harkokin wajen kasar Sergie Lavrov.

Kasashen, wadanda suke da kashi 40 cikin 100 na jama’ar duniya, na da ra'ayin bai-daya na tsarin duniya da suke ganin zai fi nuna muradunsu da samun daukaka.

Maudu’in taron karo na 15 shi ne “BRICS da Afirka” kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da nahiyar ke neman komawa fagen daga inda Amurka da Rasha da China duk suke son neman kulla kawancen diflomasiyya da tattalin arziki da yankin.

TRT Afrika