Sama da mutane 40 ne suka mutu sakamakon hatsarin wata motar dakon gas a yankin tsakiyar kasar Laberiya, kamar yadda babban jami’in kiwon lafiya na kasar ya shaida wa kafafen yada labarai na kasar.
Tankar mai dauke da mai ta fada cikin wani rami da ke kan hanyar Totota mai tazarar kilomita 130 daga Monrovia babban birnin kasar a ranar Laraba.
Dakta Francis Kateh ya shaida wa gidan talabijin na Super Bongese TV cewa zai yi wuya a iya tantance adadin wadanda hatsarin ya rutsa da su domin wasu sun kone kurmus, sai dai ya yi kiyasin cewa mutane sama da 40 ne suka mutu.
"Muna da tawagarmu da ke bi zuwa gida-gida don duba wadanda suka bata," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Kwashe man iskar gas
Da farko dai ‘yan sanda sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai 15 kuma sun ce akalla mutane 30 ne suka jikkata yayin da mazauna yankin suka taru a wurin.
"Mutane da dama ne suka kone," in ji Prince B. Mulbah, mataimakin sufeto-janar na 'yan sandan kasar Laberiya.
Wani dan sanda mai suna Malvin Sackor, ya ce bayan hadarin, wasu mutanen yankin sun rika kwasar gas din da ya malala abin da ya sa tankar ta kama da wuta, inda mutane dama suka mutu yayin da wasu kuma suka jikkata.
Ya ce har yanzu ‘yan sanda na ci gaba da tattara adadin wadanda suka jikkata da wadanda suka mutu.
Mutane sun hau kan babbar motar
Wani ganau daga garin Totota, Aaron Massaquoi, ya ce "mutane sun hau kan babbar motar da ke dauke da gas din, yayin da wasu daga cikinsu suka dauki karafa suka yi ta bugun tankar don ta fashe su samu damar diban gas din."
"Mutane da dama ne suka kewaye babbar motar kuma direban motar ya shaida musu cewa gas ne a ciki kuma zai iya tashi da wuta idan ba su yi a hankali ba," in ji Massaquoi.
“Ya ce musu kada su hau kan motar dakon man, su daina bugun tankar....amma wasu ma suna amfani da karfen kwance noti wajen yin ramuka a jikin tankar,'' in ji shi.
Hatsarin motar tankar da ya auku a kasar Laberiya na zuwa ne mako daya bayan tashin gobara a wata babbar ma'ajiyar mai a kasar Guinea inda mutane 24 suka mutu kana 454 suka jikkata