Shugaban Rasha Vladimir Putin ya karɓi baƙuncin Shugaban Mali Assimi Goita a Saint Petersburg a Yulin 2023. / Hoto: Reuters

Kasashen Mali da Rasha a ranar Juma'a sun ƙaddamar da ginin tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana mafi girma a Yammacin Afirka, kamar yadda Ministar Makamashi ta Mali Bintou Camara ta bayyana a gidan talabijin ɗin ƙasar.

Wannan na zuwa ne a yayin da ƙasar ke ci gaba da fama da tsananin rashin wutar lantarki.

"Tashar lantarkin, wadda ita ce ta ɗaya a girma a ƙasar da kuma yankin, za ta taimaka matuƙa wurin rage matsalar ƙarancin lantarkin da ake fama da ita a ƙasarmu," kamar yadda Camara ta shaida wa gidan talabijin ɗin Mali na ORTM.

Grigory Nazarov, daraktan kamfanin Novawind, kamfanin kasar Rasha mai kula da aikin, ya ce ana sa ran lantarkin da Mali ke amfani da ita za ta ƙaru da kaso goma cikin 100.

Shekara guda ana aiki

Novawind wani reshe ne na hukumar Nukiliya ta Rasha Rosatom.

Tashar wutar lantarki mai karfin megawatt 200 za ta shafe girman kadada 314 a Sanankoroba da ke kudu maso yammacin Mali kusa da Bamako babban birnin kasar.

Aikin, wanda za a kashe sama da Euro miliyan 200 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 217, zai dauki shekara guda ana gudanar da shi, in ji Nazarov.

Matsalar lantarki

Sakamakon irin bashin da ya yi wa Mali katutu na sama da dalar Amurka miliyan 330, kamfanin samar da makamashi na kasar Mali ya daina samar da wutar lantarki a babban birnin kasar da sauran garuruwan kasar.

A ranar 28 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni ne aka tsara za a fara aikin gina wasu kamfanonin samar da lantarki ta hanyar hasken rana guda biyu a kusa da birnin Bamako, kuma kamfanonin China da Masar za su gina su.

Moscow ta ci gaba da samun tasiri a Mali ta hanyar tura sojojin haya na Wagner, inda take hakan a bayan fage domin biyan muradun fadar Kremlin tun daga shekarar 2010.

A yayin wata waya da suka yi a watan Maris, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da gwamnatin mulkin sojan Mali, Kanar Assimi Goita, sun tattauna kan karfafa "hadin kai a ayyukan makamashi, aikin gona da ma'adinai", in ji Kremlin.

AFP