Gwamna Uba Sani ya ce an ɗauki matakan ne a “ƙoƙarin da gwamnatin ke yi tuƙuru wajen magance matsalolin tsaro da suke yi wa fannin ilimi dabaibayi." / Hoto:Uba Sani FB

Gwamnatin Kaduna ta sanar da wasu sabbin matakai na bai wa makarantun jihar tsaro saboda yawan hare-haren da suke fuskanta da kuma satar ɗalibai.

Gwamna Uba Sani ya ce an ɗauki matakan ne a “ƙoƙarin da gwamnatin ke yi tuƙuru wajen magance matsalolin tsaro da suke yi wa fannin ilimi dabaibayi,” kamar yadda saƙon da ya wallafa a shafin X ya ƙunsa.

A cewar gwamnan, Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da suka fi fama rikicin ‘yan bindiga da ta’addanci da sauran miyagun ayyuka.

Duk waɗannan jawabai Gwamna Uba ya yi su ne a taron horarwa da aka yi wa makarantun ‘yan sanda, da nufin ƙarfafa tsaro da bai wa fannin ilimi kariya.

“Gwamnatin jihar Kaduna na aiwatar da shirin SAFE SCHOOL domin karfafa tsaro a makarantun firamare da sakandare ta hanyar hadin gwiwa da rundunar ‘yan sandan Nijeriya,” ya ce.

Ga dai jerin matakan da Gwamnatin Jihar Kadunan ta ɗauka don kare makarantu da ilimi:

- Katange makarantu

- Haɗe wasu makantu waje ɗaya da sauya wa wasu matsugunai

- Kafa Kwamitocin Kai Agajin Gaggawa a fannin Tsaro inda za a zaɓo mambobin kwamitin daga makarantu da al'ummomin yankin

- Girke jami’an sa-kai na Kaduna KADVS zuwa makarantu - Samar da layin waya na gaggawa a makarantu

- Horon Wayar da Kan Tsaro ga Shugabannin Makarantu da malamai da sauran ma'aikatan makarantu

- Gina wuraren taruwar gaggawa a makarantu idan wani abu ya bijiro

- Horo kan yadda za a gane alamun barazana

- Gina hasumayar sa ido a makarantu.