Ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso na fama da takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba musu. / Hoto: ECOWAS

Shugabannin ƙasashen ECOWAS na gudanar da taro a ranar Asabar a Abuja domin tattaunawa kan irin ƙalubalen da yankin ke fuskanta da kuma kira ga ƙasashen ƙungiyar uku waɗanda suka yanke hukuncin ficewa sake tunani kan matsayarsu.

Taron kungiyar kasashe 15 na ECOWAS a Abuja babban birnin Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar barazana ga makomar kungiyar mai shekaru 49 a daidai lokacin da take fama da yiwuwar tarwatsewa da kuma karuwar juyin mulkin da aka yi a baya bayan nan sakamakon rashin gamsuwa kan yadda zababbun gwamnatoci ke gudanar da mulkinsu a yankin.

Babban abin da ke gabansu shi ne shawarar da Mali, Burkina Faso da Nijar suka yanke a baya-bayan nan ta ficewa daga ECOWAS, ko kuma kungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka, kan "takunkuman da ba a taba gani ba", tun bayan da aka kafa kungiyar a shekarar 1975.

"Dole ne mu sake nazari kan hanyar da muka ɗauka ta neman tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashe mambobinsu,” in ji Tinubu.

“Saboda haka ina kira a gare su da su sake nazari dangane da matakinsu na ficewa daga gidansu haka kuma kada su ɗauki ƙungiyarmu a matsayin abokiyar gaba,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Ana kuma sa ran taron zai yi nazari kan tsauraran takunkuman da aka kakabawa Nijar.

A wannan makon, daya daga cikin jagororin kafa kungiyar kuma tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya Yakubu Gowon ya bukaci shugabannin yankin da su ɗage takunkumin da aka kakabawa ƙasashen, inda ya ce ƙungiyar ta wuce haɗakar ƙasashe domin a cewarsa ta zama wata al’umma ɗaya.

AP