Burna Boy na da aƙalla mabiya miliyan 40 a shafukansa na sada zumunta a intanet wato Facebook da Tiktok da X. Hoto: AFP 

Daga Brian Okoth

A wajenku, sunansa Burna Boy, amma ga gwamnati da sauran hukumomin duniya, an san shi ne da sunansa na haihuwa wato Damini Ebunoluwa Ogulu.

An haifi mawaƙin a ranar 2 ga watan Yuli na shekarar 1991, a garin Fatakwal da ke jihar Rivers a kudancin Nijeriya.

Burna Boy, wanda iyayensa suka haifi ‘ya’ya uku, shi ne ƙadai namiji a wajen mahaifansa, sannan ya taso ne a gida na masu matsakaicin arziki.

Sai a shekarar 2012 ne mutane da dama suka soma sanin waye Burna Boy, amma rayuwarsa a waƙa ta soma ne tun yana ɗan shekara 10.

Burna Boy ya fara nuna sha'awar yin waƙa ne tun yana ƙarami. / Hoto : AFP 

Sha'awar waƙa

Ko da yake iyayensa sun amince da sha'awarsa ta yin waƙa, amma sun faɗa masa cewa sai ya kammala karatunsa tukunna.

Burna Boy ya yi makarantar firamare mai zaman kanta a garin Fatakwal sannan ya shiga makarantar sakandare a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Nijeriya. Ya kuma kammala karatunsa na sakandare a shekarar 2008.

Mahaifiyar Burna Boy, Bose Ogulu, wacce kuma ita ce manajarsa, a wata hira da aka yi da ita kwanakin baya ta bayyana cewa a lokacin kuruciyar Burna Boy, yakan zauna kusa da kakansa domin sauraron ire-iren waƙoƙin gargajiya.

A lokacin kakansa shi ne manajan fitaccen mawaƙin Afrobeat, Fela Kuti.

Mahaifiyar Burna Boy Bose Ogulu ita ce manajarsa. / Hoto: Reuters

Sa hannu a kamfanin Aristokrat Records

Bayan kammala karatun sakandare, iyayen Burna Boy sun sanya shi a Jami'ar Sussex da ke ƙasar Birtaniya don yin karatun digirinsa na farko a fannin fasahar watsa labarai.

A shekarar 2009 ne aka mayar da Burna Boy zuwa Jami'ar Oxford Brookes don kammala karatunsa a fannin sadarwa.

A 2010, mawaƙin ya koma Nijeriya inda ya samu horo na sanin aiki na shekara ɗaya a wani gidan rediyo da ke Fatakwal.

A lokacin horon ne ya ba da ƙarfinsa ga yin waƙa, daga nan ne ya sanya hannu da kamfanin Aristokrat Records.

Burna Boy na da aƙalla kundin waƙoƙi guda biyar. / Hoto: AFP

Kafa kamfanin kansa

A 2012 ne waƙar "Like to Party" ta sa Burna Boy ya shahara. Waƙar ta zama bakandamiya a kundinsa mai suna "LI.F.E" wanda ya fitar a 2013.

"Yawa Dey", "Always Love You", "Run My Race", da "Tonight" na cikin sauran fitattun waƙoƙin da ke cikin kundin.

Wakar "Yawa dey" ce ta fito da Burna Boy a sauran ƙasashen Afirka.

A farkon shekarar 2015, mawaƙin ya bar kamfanin Aristokrat Records kana ya kafa nasa kamfanin mai suna 'Spaceship Entertainment.'

Burna Boy ya kafa kamfaninsa na wakoƙi mai suna Spaceship Entertainment, a shekarar 2015. / Hoto: Reuters

Ya sayar da dukka tikitin ɗin shiga Wembley Arena

A ƙarƙashin kamfaninsa, ya fitar da aƙalla kundin albam huɗu, waɗanda suka samu nasara sosai.

A shekarar 2019, Burna Boy ya zama mawaƙin Afrobeats na farko da ya sayar da tikitin shiga kallon shirin kai-tsaye na Wembley da ke birnin London a ƙasar Birtaniya.

Kundin waƙoƙinsa na huɗu mai suna "African Giant", wanda ya fitar a watan Yulin 2019, ya haɗa wakoki da suka yi fice irin su "Gbona" da "On the Low" da "Anybody", da sauransu.

An zabi kundin a cikin waɗanda aka tattaro da suka yi fice don samun lambar yabo a matakin 'Best World Music Album category' na Grammy a 2020.

Sai dai mawaƙiya 'yar ƙasar Benin Anjelique Kidjo ce ta lashe kyautar.

Burna Boy ya yi soyyarya da mawaƙiyar Birtaniya Stefflon Don a mastayin budurwarsa . / Hoto: AFP

Wanda ya lashe kyautar Grammy

Kazalika a wannan shekarar ne, Burna Boy ya fitar da kundin waƙoƙinsa na biyar mai taken "Twice as Tall". Kundin ya lashe kyautar 'Best World Music Album' na Grammy a 2021.

Mawaƙin ya yi soyayya da mawaƙiyar Birtaniya Stefflon Don, amma alaƙarsu ta zo ƙarshe a 2021 bayan shafe tsawon shekaru uku suna tare.

Burna Boy, wanda ke da aƙalla mabiya miliyan 40 a shafukan Facebook da Instagram da TikTok da kuma X, ya samu lambobin yabo sama da 60 na a fagen sana'arsa ta waƙa da nishaɗi.

TRT Afrika