'Yar wasan Afirka ta Kudu mai kama da Ronaldinho ta dauki hankalin duniya

'Yar wasan Afirka ta Kudu mai kama da Ronaldinho ta dauki hankalin duniya

'Yar wasan Afirka ta Kudu Miche Minnies tana kama sosai da shahararren dan wasan Brazil Ronaldinho.
Miche Minnies, mai shekara 21, ta ja hankalin duniya kan yadda take kama sosai da dan wasan Brazil Ronaldinho, mai shekara 43. / Hoto: Screengrab

Daga Brian Okoth

'Yar wasan Afirka ta Kudu Miche Desiree Minnies tana kama sosai da shahararren dan wasan Brazil Ronaldinho Gaucho kuma jama'a sun lura da haka.

An fara ganin kamanninsu ne bayan da wata kafar yada labaran wasanni mai suna 433 ta rubuta a shafin Instagram cewa Minnies, mai shekara 21, ta sa ana tunawa da "wani."

Fiye da masu amfani da shafin Instagram din 7,000 ne suka gasgata hakan cewa Minnes tana kama da Ronaldinho, wanda ya lashe Kofin Duniya da kyautar Ballon d'Or da Zakaran Dan Kwallon FIFA na shekara da Kofin Zakarun Turai a tsawon shekara 20 da ya yi yana taka leda.

Minnies tana wasa a matsayin 'yar wasan gaba a kungiyar Mamelodi Sundowns Ladies da ke birnin Pretoria, kungiyar tana buga babbar gasar mata a Afirka ta Kudu.

A shekarar 2018, 'yar wasar tana cikin tawagar da ta wakilci Afirka ta Kudu a Gasar Kofin Duniya ta Mata 'Yan kasa da shekara 17 a Uruguay.

Ba ta da alaka da Ronaldinho

A kakar shekarar 2021 zuwa 2022, Minnies ta ciyo wa Sundowns Ladies kwallo 22 wanda hakan ya sa kungiyar ta lashe Kofin Lig din a karo na biyar.

Ita ce ta zo ta biyu a jerin 'yan wasan da suka fi zura kwallaye a raga, Boitumelo Rabale, wacce ita ma take wasa a kungiyar Sundowns Ladies, ita ce ta zo ta daya wadda ta zura kwallo 24.

Wasu magoya bayan Ronaldinho, mai shekara 43 a duniya, sun bukaci da a yi gwajin kwayoyin halitta na DNA don a tabbatar ko yana da alaka da Minnies.

Takardun haihuwa sun nuna cewa an haifi Minnies ne a ranar 14 ga watan Nuwamban shekarar 2001 a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, kuma ba ta da wata alaka ta jini da tsohon dan wasan Barcelona da AC Milan da kuma PSG.

Kafin ta koma Sundowns Ladies a watan Maris din 2022 kan yarjejeniyar shekara hudu, Minnies tana wasa ne a kungiyar RSA Vasco Da Gama, wato wata kungiya wacce ba ta kai matakin kwararru ba.

Wacce ta fi zura kwallaye a raga

A kakar 2020 zuwa 2022 yawan kwallon da ta zura a raga ya taimaka wa Vasco Da Gama wajen lashe kofin lig din mata kuma hakan ya sa kungiyar ta dare matakin lig din kwararru.

Yayin da take barin Vasco Da Gama zuwa Sundowns Ladies, kocin Minnies na lokacin Ashraf Calvert ya ce "ina jin dadin yadda na taimaka wa 'yar wasan wajen cimma burinta."

Kungiyar Sundowns, karkashin jagorancin Koci Jerry Tshabalala ta samu nasara har a wajen Afirka ta Kudu.

Kungiyar ta lashe Kofin Council of Southern Africa Football Associations (COSAFA) Women’s Champions League a 2021 da kuma Kofin Zakarun Afirka na Mata wato CAF Women’s Champions League shi ma a 2021.

A shekarar 2022, kungiyar ta kai wasan karshe a duka gasar biyu kuma ta kasance wacce ta zo ta biyu.

TRT Afrika