Mai yiwuwa a tilasta wa mutane miliyan 38.5 su yi ƙaura a tsakanin ƙasashen masu maƙwabtaka da teku sakamakon sauyin yanayi zuwa shekarar 2050.  / Hoto: AFP Daga Gift Dumedah      

Daga Gift Dumedah

A babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na shekara-shekara karo na 28 (COP28) da ake gudanarwa a Dubai, mahalarta sun amince su tafiyar da Gidauniyar Tallafawa Ƙasashe Masu Fama Da Mummunan Tasirin Sauyin Yanayi, su taimaka wa ƙasashe masu tasowa da ke fama da mummunan tasirin sauyin yanayi.

An yaba wa wannan sanarwar a matsayin yarjejeniya mai cike da tarihi, musamman ma rashin fayyace abin da gidauniyar tallafin ke nufi, da kuma ƙin aminta da tabbatar da ita, musamman wanda mafi yawa daga ƙasashen da suka ci-gaba suka yi.

An gano cewa "Asara da Lahani" wani mummunan sakamakon sauyin yanayi ne na tattalin arziƙi ko ba na tattalin arziƙi ba, da ke faruwa ko akwai ko babu matakan taƙaita al'amura ko sauya ɗabi'un mu'amala da muhalli.

Saboda da haka, ana sa ran Gidauniyar Tallafawa Ƙasashen Masu Fama Da Mummunan Tasirin Sauyin Yanayin za ta samar da tallafi don magance mummunan tasirin sauyin yanayi, kamar rasa fili, da gine-ginen da kuma hanyoyin cin-abinci, sannan ta bai wa ƙasashe masu tasowa diya kan mummunan tasirin sauyin yanayi.

Ko shakka babu, ya kamata manyan masu fitar da gurɓatacciyar iska da kuma ƙasashen da suka ci-gaba su amince da alhakin sanin ya kamata da ke wuyansu, su bai wa gidauniyar gudummawa. Abin ƙarfafa guiwa ne cewa akwai wani yunƙuri da ake yi ta wannan ɓangaren, wanda akwai buƙatar saura su yi koyi da shi.

A Wajen al'ummomi a Afrika da ke fama da munanan tasiri iri iri sakamakon kasadar sauyin yanayi da ba za a iya kauce mata ba, kamar tunkuɗowar teku da kuma matsanancin sauye sauyen yanayi, mene ne tasirin wannan Gidauniyar Tallafawa Ƙasashen Masu Fama Da Mummunan Tasirin Sauyin Yanayin?

An yadda a faɗin duniya cewa, illahirin adadin gurɓatacciyar Iskar da Afrika ke fitarwa na kimanin kashi 4 ƙanƙani ne idan aka kwatanta da gurɓatacciyar iskar da sauran nahiyoyin ke fitarwa, amma kuma ita ce ke fama da munanan tasirin sauyin yanayi.

Daga cikin sakamako sauyin yanayi masu lahani, raba mutane da muhallansu sakamakon sauyin yanayi yana na gaba gaba a ƙasashen Afrika da ke gaɓar teku, abin da galibi ke haddasa ƙaurar jama'a a gida da waje.

Matakai Daban-Daban

A cewar wasu hasashe, mai yiwuwa a tilasta wa mutane miliyan 38.5 su yi ƙaura a tsakanin ƙasashen masu maƙwabtaka da teku sakamakon sauyin yanayi zuwa shekarar 2050.

Girman matsalar barin muhalli sakamakon sauyin yanayi na nufin cewa, wannan gidauniyar za ta zama mai matuƙar muhimmanci wajen samar da sa'ida ga ƴan Afrika da sauyin yanayi ya raba da muhallansu masu ƙaruwa, har da waɗanda ke zaune a yankunan da ke maƙwabtaka da teku.

Ana sa ran gidauniyar ta samar da kuɗin da ba bashi ba cikin hanzari wa ƴan Afrika da sauyin yanayi da ke ƙara bazuwa ya raba da muhallansu, in ji kundin COP28.

 Akwai buƙatar sauyin yanayi a yankunan teku na Afrika a magance shi ta hanyar amfani da halittu min Indil Lahi./Hoto AA

Asara da Lahani da sauyin yanayi ke jawowa babbar matsala ce, amma kuma, ita ma ɗaya ce daga cikin ƙalubale iri-iri da ke addabar al'ummomin Afrika mazauna yankuna masu maƙwabtaka da teku.

An yarda cewa matakai na gaba ɗaya kuma masu ɓangarorin barkatai da suka ƙunshi masalahohi ta yin amfani da halittun min indil Lahi, da sauya ɗabi'u wajen mu'amala da muhalli, da taƙaitawa da juriya, da daidaito da ɗorewa da kuma aiki tare, ana buƙatar su, domin a iya magance ƙaura sakamakon sauyin yanayi a Afrika.

Wannan, ta wata fuskar, yana samuwa ne sakamakon tasiri mai sarƙaƙiya tsakanin sauyin yanayi da al'ummomi, da muhalli da kuma rashin iya sabawa da wani yanayi sosai a Afrika, da ke buƙatar mayar da hankali kan masalaha mai inganci da zata kawo ƙarshen ƙalubalen da ƙaura sakamakon sauyin yanayi ke haddasa wa.

Yankin Afrika da ke maƙwabtaka da teku na ɗauke da babban kaso na yawan jama'a na nahiyar, muhimmin yanki ne ta fuskar tattalin arziƙi da zamantakewa da ya zama jigo ga tattalin arziƙin ƙasashe dayawa, kuma yana da muhalli mai sauƙin fuskantar matsala, da da halittu da mazauninsu da kuma albarkatu da suka haɗa da ƙananan halittun cikin ruwa, da wuraren da ruwa ya mamaye, da wurare masu danshi da sauransu da yawa.

Duba da muhimmancinsa, ya wajaba a ce, karewa da kuma farfaɗo da yankin Afirka da ke maƙwabtaka da teku, ya wuce batun Gidauniyar Tallafawa Ƙasashen Masu Fama Da Mummunan Tasiri Sakamakon Sauyin Yanayi.

Zaɓi mai ɗorewa

Haƙiƙanin gaskiya, akwai matsaloli da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa da ke addabar yankin Afrika da ke maƙwabtaka da teku, waɗanda wasunsu ke da alaƙa da tunkuɗowar teku da ambaliya,da zaizayewar ƙasa gurɓatar muhalli (iska, ruwa da ƙasa), mamayar ruwan gishiri da kuma aikace-aikacen bil'adama kamar kwasar yashi.

Manya manyan matakai sha-kundum kuma masu yawa na buƙatar raya mazaunin halittu, waɗanda wasunsu sun zarci iyakokin ƙasashe, tare da bayar da muhimmanci wa manyan matakai.

Matakin rage gurɓatacciyar iska a yankunan Afrika da ke maƙwabtaka da teku na buƙatar ya kasance, ta yin amfani da halittu min indil Lahi, tare da bayar da muhimmanci ga wasu halittu da matakai da za su ɗore, wajen maido da muhallin halittun da ke ƙasashen da ke gaɓar teku.

Wannan ba za a iya cim masa ba ba tare da yin ɗawainiya wajen sauya ɗabi'u a mu'amala da muhalli, da taƙaita alamura da kuma nuna juriya - waɗanda sune ya kamata Gidauniyar Tallafi ta ƙasashen da ke fama da mummunan tasirin sauyin yanayi ta bai wa muhimmanci.

Har Ila yau, ana buƙatar daidaitattun matakai masu ɗorewa domin tabbatar da cewa an kare duk mutane da al'ummomi ta fuskar tattalin arziƙi da zamantakewa da al'ada yayin farfaɗo da muhallin halittu da ya gurɓace.

Wajibi ne a goyi bayan hakan ta hanyar aiki tare da haɗin guiwa mai karsashi kuma tsakani da Allah, don tabbatar da cewa, al'ummomi mazauna waje ne suka mallaki waɗannan shirye shiryen kuma suke gudanar da su.

Idan aka dubi yanayin da sauyin yanayi ke bujirowa, ya kamata wani cikakken tsari na ankararwa a kan lokaci, tare da tsarin zamantakewa da tattalin arziƙi a haɗe su waje guda domin kare jin daɗin rayuwar jama'a.

Marubucin, Gift Dumedah, masani ne dan ƙasar Ghana, wanda aikin bincikensa ya mayar da hankali kan ruwa da yanayi da kuma muhalli duniya.

Hattara Dai: Ra'ayoyin da marubuciyar ta bayyana ba dole ba ne ya kasance daidai da ra'ayi, da hange da nazari da kuma manufofin editan TRT Afrika ba.

TRT Afrika