Mawaƙiyar ƴar asalin Colarado ta bayyana irin darussan da ta samu dangane da Musulunci sakamakon azumin da ta yi. / Hoto: Others

Daga Elizabeth Herriman

Sakamakon na girma bayan harin 11 ga watan Satumba, a matsayin wadda ba musulma ba Amurka, ni ba bakuwa ba ce kan kin jinin Addinin Musulunci.

Tun daga kallon shirin Jeff Dunham tare da yar tsanarsa, da Achmed the Dead Terrorist on Comedy Central, da ganin yadda mutanen da ke kusa da ni suka yarda da jita-jitar cewa tsohon shugaban Amurka Barack Obama Musulmi ne a asirce, da kuma jin yadda yaran ajinmu suke ihu suna cewa “Allahu Akbar” tare da shagube kan 'yan kunar bakin wake – yin izgilanci da cin mutuncin Musulmai wani abu ne da aka saba yi a ko'ina a fadin Amurka.

Wannan dangantaka manuniya ce da kuma salon da wasu ‘yan siyasa ke amfani wajen ingiza yaki da tashe-tashen hankula a wasu kasashe cikin sauki.

Tasirin hakan na fitowa fili karara, kamar yadda muka ga kyamar Addinin Musulumci ke taka rawa a kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa a Gaza.

Masu goyon bayan Falasɗinawa sun taru a dandalin New York Times a ranar 30 a watan Maris ɗin 2024. / (AFP/Leonardo Munoz)

Mutane da dama a Amurka suna danganta Addinin Musulunci da mabiyansa da tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya, duk da cewa addini ne da ya bambanta da mabiyansa daga ko'ina a fadin duniya.

Tun abubuwan da suka faru a ranar 7 ga watan Oktoba, ni, kamar sauran al’ummar Amurka, muka fara zurfafa bincike tare da neman ilimi game da rikice-rikicen da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, a karon farko na yi bincike da kaina.

Abin da na gano shi ne, ba na jin dadin yadda gwamnati ta ke amfani da dalolin harajina wajen daukar nauyin kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ba wani abin mamaki bane, kamar sauran ’yan uwana Amurkawa, na fara kaurace wa kamfanoni don rage kudaden shigarsu da kuma kakaba musu jerin takunkumi (BDS), a kokarin da nake na cire kudina daga aljihun mutanen da ke da manufar amfani da su wajen tashin hankali.

Abin da na koya a lokacin shi ne, a cikin ƙasar da al'adun samun kudaden shigarta ya ginu ta hanyar amfani da kayayyaki da take samarwa, yana da wuya a daina kashe kuɗi.

A daidai lokacin kuma na soma gwagwarmaya tsakanin dabi'u na da karfin sha'awata, daga nan na fara ganin sakonnin shirye-shiryen Musulmai na azumin watan Ramadan a kan TikTok.

Yayin da nake bincike kan bayanai game da Ramadan, na samu ainihin dabi'un watan mai alfarma wandanda suka ƙunshi abubuwan da nake ƙoƙarin yi wa kaina.

Don haka sai na yanke shawarar yin azumi na watan Ramadan a matsayina na wanda ba musulma ba domin in ga abin da zan koya daga cikin watan. Lokacin da na shirya bidiyon TikTok dina na farko kan Ramadan kuma na wallafa shi a shafina, ina da mabiya 300.

A yanzu haka shafina ya karu zuwa mabiya 20,000 tun bayan wallafa wannan bidiyon. Ina fatan zan samu ƙarin mutane da ke gwagwarmaya irin nawa. Ina kara musu kwarin guiwa kan su je su samu ilimi tare da koyi kan addinin da ake yawan batawa a kafafen yada labarai namu.

Bidiyon na farko ya kare da taba jama’a da dama, musulmai da ma wadanda ba musulmai ba.

Tun da farko ban shirya hada jerin bidiyon ba, amma da wasu masu sharhi suka ba da shawarar yin hakan, sai na ga wata dama ce ta yakar wani batu da nake gani a lokacin da nake fafutukar samun ‘yancin Falasdinu.

A lokuta da dama, mutanen da na sani suna danganta Musulmai da Addinin Musulunci da Hamas da ayyukan ta'addanci. Wannan batu na cewa idan kai Musulmi ne ko daga yankin Gabas ta Tsakiya, to, kai dan ta'adda ne, ba sabon abu ba ne.

Elizabeth ta ce ta koyi yin azumi a matsayinta na wadda ba Musulma ba a lokacin watan Ramadana. / Others

Farfagandar da ake yadawa game da Musulunci da kuma abin da mabiyansa wadanda ake zargin suna goyon bayan tayar da tarzoma a tsawon watanni shida da suka wuce yayin da ake kai wa Gaza hare-haren bama-bamai. A mafi yawan lokuta ina ganin mutane suna amfani da kyamar musulunci wajen tabbatar da hakan.

Daga cikin ire-iren kalamai karfafa gwiwa da na samu daga mutanen da suka kalli bidiyona, akwai wasu da suka soke yanda aka saba kallon musulunci.

Don haka na yanke shawarar cewa, yayin da nake azumin Ramadan, ina so in ba da labari kan abubuwan da ji da kuma yin wasu bidiyoyin da su yaƙi rashin fahimta game da addinin.

Ya zuwa yanzu na ba da sadaka, na karanta wasu shafuka daga cikin Alqur'ani, na gwada sanya hijabi, na yada bayanai game da gaskiyar addinin Musulunci da dukkan kyawawan ayyukan mutanen da ke cikin addinin, kuma na samu karbuwa da kalamai masu dadi.

Na hadu da al'umma mafi karamci da aminci wadanda ban taɓa haduwa da su ba a tsawon rayuwata. Irin soyayyar da al'ummar musulmai suka nuna min ta zarce duk wani suka da aka min a baya.

Kawata da danginta sun taimaka min sosai, hakan ya zama min alheri. Kazalika, na samu damar amfani da sabon dandalina don yin magana game da abin da ya shafi Falasdinu da kuma taimakawa wajen raba kudade don kwashe iyalai daga Gaza da kuma jaddada muhimmanci a tsagaita wuta na din-din-din.

Azumi yana da wahala amma yana da lada. Kowa yana gaya min cewa kwanaki ukun farko za su fi wahala, kuma sun yi gaskiya. Waɗannan ƴan kwanaki na farko, na fi jin yunwa da rana sosai, kuma ban tabbatar ko zan iya yin cikakken azumin watan ba.

Amma daga ƙarshe, bayan na samu damar yin buɗe baki, nakan ji daɗin samun abinci da ruwa fiye da yadda na saba a baya. Ina jin daɗin yanayin kuma na samu kwarin gwiwa a kan iya horon kaina.

A wannan lokaci na watan Ramadan, azumin rana yana da sauki sosai, kuma na fi mayar da hankali wajen bayar da gudummawa ga sauran al'amuran watan mai alfarma, don haka ina neman karin hanyoyin da zan karasa azumin watan Ramadan ta hanyar taimaka wa al'ummar musulmai gwargwadon yadda suka taimaka min.

Yayin da watan Ramadan ke kokarin karewa, ina kan shirye-shirye tare da sauran masu fafutuka da kungiyoyi kamar Operation Olive Branch don amfani da kafar TikTok kai tsaye don "Daukar nauyin wani Iyali" daga Gaza da kuma taimakawa wajen daidaita gudummawar da ake bayarwa ga kamfen ɗin su na GoFundMe don su iya ƙaura daga yankin.

Yanayin da na ji a cikin wannan wata ya zarce misali kuma na koyi abubuwa da yawa daga ciki.

Ina ganin duk wanda ke da sha'awar sanin addinin Musulunci to ya je ya nema domin za ku samu karbuwa hannu biyyu- biyyu kuma dumi-duminsu za su karbe ku.

Marubuciyar, Elizabeth Herriman mawaƙiya ce, mai rubuta waka sannan mai fafutuka ce wadda ke zama tare da saurayinta da kuliyoyinsu uku a tsaunukan Colorado.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubuciyar ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika