Wasu kasashen Turai sun shahara da nuna kyamar Musulmi da Musulunci. Hoto: AA

Daga Joram Van Klaveren

Masu rajin kare akidun ‘yanci da raba gwamnatoci da addini, na amfani da ‘yancin fadin albarkacin baki wajen cin zarafin wasu addinan daban.

“Mafiya nagarta daga cikinku su ne wadanda suka fi kyawawan halaye da dabi’u.” - In ji Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW.

Abun bakin ciki, mai bata rai, kuma na zagi. Wadannan ne wasu daga cikin siffofin da za mu iya baiwa lamarin kona Alkur’ani Mai tsarki da aka samu a wasu kasashe irin su Swidin da Holan.

Wasu bata-garin ‘yan siyasa da mutanen kawai suna wasa da batun tsokanar Musulmai ta hanyar batanci ko cin zarafin littafinsu mai tsarki, saboda neman suna ko kuma son a sani.

Batun cewar akwai wawaye da masu kyamar mutane ba sabo ba ne. Abu ne da aka saba gani a koyaushe, kuma ake samu a dukkan kasashe tare da dukkan al’ummu.

Abun da yake sabo shi ne yadda ake hawan kawara da cin zarafin wani addini da wasu suke tsarkakewa – ta kai har wasu gwamnatoci ma na murna idan hakan ta faru.

Ta hanyar fake wa karkashin ‘yancin fadoin albarkcin baki, ana barin a aikata kowanne irin abu a wasu kasashen Turai a yau. Fadin albarkacin baki da bangare daya yake babatu a kai ya zama wani abu mai tsarki a wajen su.

Game da wannan batu, mung a yadda ake kona Alkur’ani Mai Tsarki - kuma ma don tsokana ana yin hakan a kusa d Masallaci, karkashin samun kariya daga ‘yan sanda.

Rasa Imani

Ya munana matuka yadda ake da la’anannun dokoki a kasashen da ke bayar da dama a kona Alkur’ani Mai Tsarki.

Zagin mutum guda, zagin mutane da yawa, bata suna, cin zarafi da yunkurin farwa mata duk laifuka ne da ake hukunta masu aikata su.

Ba a yarda wani ya zago sojoji ko ‘yan sanda ba. Zagin sarki na iya janyo wa a daure mutum tsawon watanni hudu a kurkuku a Holan, Har zuwa 2014, cin mutuncin wani addini babban laifi ne a kasar.

Wadannan ka’idoji kan fadin albarkacin baki na nuni a yadda na nuni da akwai iyaka, kuma a matsayinmu na al’umma a kyaushe muna son mu ga an saka dokar kiyaye wasu al’amurra.

Amma abun takaici lokaci ya sauya. Dalilin da ya sanya ake fadar haka shi ne yadda a yau kona Alkur’ani Mai tsarki ya fado bangaren ‘yancin fadin albarkacin baki wanda ke da alaka da batun raba gwamnati da addini a aksashen Yamma.

Tun 1970, tasirin addini a kan kasashen Turai da dama ya ragu sosai. Inda tsawon karni da dama addini ya taka rawa a rayuwar mutane, iliminsu, siyasa, dokoki, kafafan yada labarai da al’adunsu, amma abun ba haka yake ba a wannan lokaci.

Al’umma baki daya na tashi da girma ba tare da sanin addini ba, babu wasu dabi’u nagari da ke tattare da su. Matsayin addini a rayuwar yau da kullum ya dusashe, kuma muhimmancin iyalai, rike akidu masu kyau na zamantakewa sun kau.

A Holan, wannan yanayi ya jefa mutane da dama cikin zaman kadaici, ya sanya an mayar karuwanci ba komai ba, yawan amfani da kwaya kayan maye, yawan amfani da kalmomin rantsuwa a fina-finai, rayuwar karya da son duniya, mummunar dabi’ar tsiraitar da al’umma da kuma daduwar kadaici da rashin manufa a rayuwa.

Dabi’u sun mutu

Za a iya cewa yammacin duniya ba su da sauran tarbiyya mai kyau.

Tare da rasa wannan tarbiyya da ruhin addini, babu yadda za a fahimta tare da aminta da addini.

Wannan ne ya sanya mutane za su har suna da ‘yancin su kona Alkur’ani Mai Tsarki, tare da aikata wasu munanan abubuwa. Baya ga haka, idan har babu wayar da kai da tausayi, to babu yadda za a samu hali nigari.

A yau tsarin ‘yanci da watsi da addini ya zama mai nusarwa gag a aminta da tsarin da ya yi daidai da nasu kawai.

Sannan da zarar wani ya ambaci batun ilimin jima’I a makarantun firamare, batun sauyin halitta a azuzuwa, fareti tsira-tsirara a gaban jama’a, ko y ace aure batu ne tsakanin mace da namiji kawai, sai a fara tsangwamar sa ana kiran sa da wanda bai waye ba ko a fara zargin sa da mai nuna kyama ga masu neman irin jinsinsu.

Amma kuma da zarar wani ya soki Musulunci, ya muzanta Musulmai ko ya kona Alkur’ani Mai tsarki, sai a fara yi masa kallon gwarzo da ya yi abu karkashin ‘yancin bayyana ra’ayi. Kai Tuari fa ta gama bace wa daga hanya mai kyau.

Idan har kona Alkur’ani na nuni da wani abu, to lallai wannan abu shi ne tabarbarewa da lalacewar tarbiyya.

Marubicin wannan Makala, Joram van Klaveren, tsohon Mamban majalisar Dokokin Holan ne.

Mai sukar Musulunci a baya, amma daga baya ya sauya ra’ayi a loakcin da yake rubuta littafin adawa da Musulunci, kuma ya yi sanadiyyar Musuluntarsa. Shi ne ya samar da Cibiyar Fahimtar Musulunci, gidan adana kayan tarihi na Musulunci na farko a Holan.

TRT Afrika