Rashin kwakwalwa a tattare da mutum-mutumi na nufin hanyoyin ladabtarwa na gargajiya ba su da tasiri. / Hoto: AP

Daga Melike Tanberk

Dan karamin labarin da za mu bayar, labarin littafin aikata lafuka na Dostoyevsky mai suna 'Crime and Punishement' (Laifi da Hukunci), ya bayyana a zamanin da ake da sadarwar yanar gizo, sannan mu kalli izina daga babban jarumin littafin, Raskolnikov.

A wata rana ta kaddara, a yayin da lissafin RaskolnikAI ya yi sauri sosai, an fahim lallai mutumtaka na cutar da dukkan suran ababanhalitta masu rai.

Sai dai kuma, a namu salon bayanin, wanda yake jarumin ba dan adma ba ne, mutum-mutumi ne da ake kira da sunan RaskolnikAI. An samar da shi da fasahar ds zai iya aiki da yanke hukunci, Raskolnik AI na aiki da bayar da sakamako, inda yake gne abu mai kyau da sakamakon da aikin yake bayarwa.

Don haka, a wata manuba da aka gididdige, ya samar da jerin wasu ayyuka da ke da manufar dalilin - samar da shi don inganta jin dadin dabbobi, tsirrai a muhalli don kara yawan farin ciki.

Bayan samun karfin gwoiwa daga wannan manufa, sai ya fara kawar da 'yan adam tare da Gatari- tunanin da aka gano gatari, wanda shi ne makamin da Dostoyebsky ya zaba - a duk lokacin da dama ta samu.

Sannan kuma, kwararru su kafa hujja da al'amarin da ya faru, yawaitar zargi game da saka hannun Kirkirarriyar Basira. Sun gano alakar wannan aiki da RaskolniKAI .

Amma tambayar ita ce, ta yaya wani zai takura wa mutum-mutumi ya tunkari illar da zabin d ayake da shi za su janyo?

Dokokin amfani da kirkirarriyar basira

Maganar samar da dokokin amfani da kirkirarriyar basira na kara samun karbuwa, musamman a yanzu da mahukunta a duniya suke ta kara duba yiwuwar dabbaka dokokin kirkirarriyar basira kamar na AI Act, da AI Safety Summit da White House Executive Order da California's SB-1047.

Yunkurin nan da ake yi, sun nuna yadda ake kara samun nasara wajen tabbatar da an samar da ka’idojin amfani da kirkirarriyar basira, musamman yanzu da mutane suke nuna damuwarsu a kai.

Sabani wajen samar da dokokin a tsakanin Turai da Amurka da kasashen G7 sun taimaka wajen rashin daidaito, wanda hakan ya kara haifar da muhawara a kan hakinanin ka’idojin da suka fi dacewa.

Mahukunta a Turai suna ta kokarin ganin sun assasa ka’idar da za ta karade duniya, wanda ya kunshi kula da bayanan sirri, a dayan bangaren kuma Amurka na kokarin kalubantar Turan wajen samar da nata dokokin daban.

Duk da haka, duk da cewa da kamar wuya samun matsala wajen fitar da dokokin, musamman duba da ita ma kasa kamar China, wadda ita me take da karfin fada-a-ji tana da wata fahimtar daban.

Sannan samar da kirkirarriyar basirar harsuna wato LLMs kamar ChatGPT sun kawo wani sabon tsaikon, inda suka jawo wata muhawarar kan kula da yadda suke gudanar da aiki.

Yadda ake samun wuce gona da iri ya sa dole a samar da dokoki masu karfi a kan amfani da kirkirarriyar basirar harsunan, duk da cewa ba laifi a dan daga kafa kan wasu kanana daga cikinsu, amma ba wai a barsu kara zube ba.

A daidai lokacin da ake cigaba da wannan tattaunawarsa, babbar matsalar da ake tunani ita ce ba kirkirarren mutum-mutumi damar kamar mutum.

Wannan lamari ne da yake bukatar natsuwa kafin daukar mataki, domin akwai matsalolin da suka jibinci bibiya da sauransu, wanda hakan ya sa ake waiwayar kirkirarren labarin mutum-mutumin Raskolnik (wanda ya gano akwai bukatar kashe mutanen duniya).

Shin wadanda suke kirkire shi ne, ko masu amfani das hi, ko shi kan shi ne za a kama da laifi idan aka samu matsala? Wannan tambayar na bukatar amsar gaggawa.

Akwai wasu ka’idoji a yanzu haka, amma ko kadan ba za su wadatar ba musamman rashin hanyoyin bibiyar ayyukan kirkirarrun basirar.

Misali a wuraren da kirkirarrirar basirar ta yi yunkurin aikata wani laifi da gangan, sannan ta aikata laifin, matsalar ta fi cabewa, saboda tambayar a nan ita ce waye mai laifin, kuma wane irin hukunci za a yi masa.

Rahotanni na kusa-kusan nan daga wasu hukumomi irin su Cibiyar Binciken Laifuffuka ta Majalisar Dinkin Duniya wato United Nations Interregional Crime and Justice Research Institute (UNICRI) da Cibiyar Binciken Laifuffukan Yanar Gizo wato Europol's European Cybercrime Centre (EC3) sun bayyana bukatar a sanya kirkirarriyar basira a cikin masu yunkurin aikata laifi.

Ana amfani da kirkirarriyar basira wajen aikata laifuffuka manya da kanana, musamman ta yanar gizo. A wannan yanayin, yunkurin aikata laifin yana cikin abubuwan da mutane ne kula da shi, yayinda aikata laifin kuma daga kirkirarriyar basirar ne.

Sai dai duk da haka, wata matsalar ita ce idan ya kasance ba wai ana ingiza kirkirarriyar basirar wajen aikata laifi ba ne, ita da kanta ce take aikata laifin.

Mayar da kirkirarriyar basira tamkar mutum

Kamar yadda rahoton Majalisar Wakilan Turai na 2017 ya bayyana, akwai wani kuduri da aka gabatar na a amince da wasu na’ukan mutumin-mutumi su zama kamar mutum mai amfani da lantarki.

Da suke kafa hujja da rubutun fitattun marubuta kamar Mary Shelley, Frankenstein da the legend of Prague's Golem, rahoton ya nuna yadda mutane suke sha’awar kirkirar mutum-mutumi masu basira. Abubuwan da a baya ake zato, yanzu sun fara zama zahiri.

Sai dai abubuwan da aka yi da dama a baya ba su da alakar kai-ysaue da kirkirarriyar basira. Rahoton ya nuna cewa idan aka amince da mutum-mutumin zama mutumi mai amfani da lantarki, zai zama duk laifin da suka yi, su za a hukunta kamar yadda ake hukunta mutum ko ma’aikata.

Duk da cewa amfani kirkirarren mutum-mutumi wajen yin wani aiki yana da kyau, har yanzu kalubalen shi ne wanda zai dauki laifi idan ya yi kuskure.

Rahoto ya kara nanata cewa akwai rudani a gano yadda mutum-mutumin suke kudurce wani mataki da za su dauka, wanda wannan ne ya sa aka kasa samuan matsaya a tsakanin ’yan majalisar.

Wadannan matsalolin suna da illoli sosai. Idan ’yan majalisar suka amince da mutum-mutumin na lantarki ya rika koyon abubuwa da kan shi, kamar yadda mutane suke yi, za a samu matsala.

Har yanzu dai ba a gano yadda za a kama mutum-mutumi da laifi ba, wanda hakan bai rasa nasaba da rashin gano yadda suke gudanar da ayyukansu a zahirii, da rashin gabban sunsuna, wanda hakan ya sa hukunci a kansu zai yi wahala.

Wannan ne ya sa akwai gibi babba a wajen shari’ar da ta shafi bangaren.

Bayan haka, yadda AI din suke iya kwaikwayon wasu halaye marasa kyau sun kara jawo fargaba da bude wata kofar a tattaunawar da ake yi.

A yanzu da ake cigaba da tattaunawa batun yiwuwar mayar da AI tamkar mutum, lallai akwai bukatar a tabbatar da su a matsayinsu na mutum-mutumi, amma masu siffofi na musamman.

Ba zai yiwu ba a sanya wa wadannan kirkirarrun abubuwan dokoki irin na mutane. Misali hukuncin kisa ko zuwa fursuna ba zai hana wasu kirkirarrun basirar aikita laifi ba, domin ba za su iya gane abin da aka yi ga wasunsu ba.

Idan muka koma kan labarin kirkirarriyar basirar Rasokolnik, idan mutumin-mutumin cikin labarin ya yanke shawarar kashe al’umma, hanyoyin shawo kan lamarin sun yi karanci.

Hanya daya watakila da za a iya magance wannan matsalar ita ce lalata mutum-mutumin kafin ya koyar da takwarorinsa barnar da yake kudurin aikatawa.

Duk da hakan, kafin a farga, aikin gama y agama, domin said a barnar da suka yi ta shiga tarihin laifin kisan da kirkirarriyar basirar da suka jawo.

Dole al’umma su muhimmantar da cigaban rayuwa duk da kura-kuren da suka cikin rayuwa. Misali, kamar yadda Dostoyevsky yake cewa, “Kuskuren mutum daya da kan shi, ya fi daidai din kirkirarriyar basirar wani.”

Marubucin, Melike Tanberk, mai bincike ne a tsarin dokoki da kiyaye sirruka a kirkirarriyar basira da ke Jami’ar Cambridge. Tana kuma da digiri a falsafa daga Jami’ar Oxford.

Togaciya: ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya yi daidai da ra’ayi ko ka’idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika