Shugaba Erdogan a ranar Litinin ya ragargaji Isra'ila kan harin da ta kai Rafah a ƙarshen mako, yankin da a baya aka ayyana shi a matsayin "tudun mun tsira." / Photo: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce "harin da aka kai Rafah a ranar Lahadi, wanda ya biyo bayan umarnin Kotun Duniya, ya fallasa irin ha'inci da zubar da jini na 'yan ta'adda".

Shugaba Erdogan a ranar Litinin ya ragargaji Isra'ila kan harin da ta kai Rafah a ƙarshen mako, yankin da a baya aka ayyana shi a matsayin "tudun mun tsira."

Erdogan ya kuma yi kakkausar suka ga firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana mai cewa: Netanyahu da ke cikin rikici da kuma abokansa da suke kisan gilla tare na kokarin tsawaita lokacinsu ta hanyar yi wa mutane kisan kiyashi yayin da suka kasa yin nasara a kan gwagwarmayar Falasdinawa.

Netanyahu yana kwaikwayon masu laifin yaƙi

"Netanyahu ba zai iya ceton kansa daga kukan da ake da shi na kwaikwayon salon kisan ƙare dangi na tsohon ɗan siyasar Yugloslavia Slobodan Milosevic da Radovan Karadzic na Bosniya da kuma Adolf Hitler na Jamus," in ji shugaban.

Erdogan ya kuma jaddada cewa, Turkiyya "za ta yi duk abin da za ta iya don ganin cewa an gurfanar da wadannan mugayen Isra'ilawan a gaban kuliya bisa laifukan da suka aikata."

An kashe mutane da dama a Rafah

Akalla mutum 35 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata yayin da Isra’ila ta kai hari kan sansanin ‘yan gudun hijira da ke Rafah ranar Lahadi.

Ofishin yada labarai na Gaza ya ce harin ya afku ne a kusa da cibiyar hada kayan agaji na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA a Tal al Sultan.

Ofishin yada labaran ya ce jiragen Isra'ila sun kai hari kan tantuna da dama a yankin, inda ya kara da cewa an yi amfani da makamai masu linzami da bama-bamai masu nauyin fam 2,000.

Tun da farko, rundunar tsaron farar hula ta Gaza ta ce yankin da aka kai harin yana ɗauke dai akalla mutum 100,000 da suka rasa matsugunansu da ke samun mafaka.

TRT World