Sojojin Isra'ila sun kashe aƙalla Falasɗinawa 17 ciki har da yara fiye da 10 sun kuma jikkata wasu da damabayan sun kai hari kan wasu birane biyu a biranen Gaza da Rafah.  / Hoto: AA  

1036 GMT — Isra'ila tana sa ran cewa Kotun Duniya Kano Hukunta Manyan Laifuka za ta umarci Isra'ila ta dakatar da munanan ruwan wutar da take yi a Gaza, kamar yadda kafofin watsa labaran Isra'ila suka rawaito.

Masana shari'a sun bayyana cewa akwai yiwuwar kotun za ta ba da umarnin ranar Juma'a, kamar yadda wata majiyar diflomasiyyar Isra'ila ta shaida wa jaridar srael Hayom.

Ya ce kotun za ta iya ba da umarnin a dakatar da ayyukan soja da Isra'ila ke yi a Rafah ko ta nemi a tsagaita wuta a yaƙin da ake yi a Gaza ta hanyar umarnin kotu.

1238 GMT — Ƙwararriya a Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga Isra'ila ta binciki rahotannin cin zarafin Falasɗinawa da ake tsare da su

Wata ƙwararriya ta Majalisar Ɗinkin ɗuniya ta yi kira ga Isra'ila ta binciki zarge-zarga dama na cin zarafi da keta mutucin Falasɗinawa da ake tsare da su tun bayan harin 7 ga watan Oktoba da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar.

Wakiliyar Musamman ta Musamman ta Majalisar kan Cin Zarafi Alice Jill Edwards, ta faɗa a cikin wata sanarwa cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe na yadda ake lakaɗa wa mutane duka, da kulle mutane an rufe masu ido da kuma ɗaure musu hannaye na tsawon lokaci.

Babu martani nan take daga gwamnati ko sojojin Isra'ila kan zargin.

0830 —Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 25, ciki har da jarirai 10 a Gaza

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 17, waɗanda suka haɗa da fiye da ƙananan yara 10, sannan suka jikkata gommai a hare-haren da suka kai gidaje biyu a Birnin Gaza da Rafah.

A sansanin 'yan gudun hijira na Al-Nuseirat, sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla takwas.

Wasu ganau sun ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 16, ciki har da yara 10, kana suka jikkata mutane da dama a harin da suka kai wani gida a yankin Al-Daraj na Birnin Gaza.

Kazalika, wasu majiyoyi sun ce dakarun Isra'ila sun kashe wani Bafalasɗine yayin da suka kai hari a gidan wani mutum mai suna Al-Sha'er a Rafah da ke kudancin Gaza.

0125 GMT — Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a kusa da ofishin Netanyahu

Ɗaruruwan Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a ƙofar ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu lokacin taron majalisar ministoci ta yaƙi, suna neman a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Zanga-zanga ta kuma ɓarke a biranen Isra'ila da dama bayan an wallafa wani bidiyo da ke nuna mayaƙan Hamas sun kama wata sojan Isra'ila a wani sansanin sojoji da ke matsugunin Yahudawa na Nahl OZ a kusa da katangar Gaza a ranar 7 ga Oktoban bara.

A cikin wata sanarwa, Hamas ta ce "an jirkita bidiyon wanda ake yaɗawa a kafofin watsa labaran Isra'ila sannan ba ma za a iya tabbatar da sahihancinsa ba."

Ta ƙara da cewa "yaɗa bidiyon na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta gaza ɓata sunanmu ta hanyar yaɗa labaran da aka ƙirƙira da aka tabbatar da cewa na ƙarya ne, ta hanyar kafofin watsa labarai da dama da kuma bincikin da kafofin watsa labarai suka dinga yi."

Wata jaridar Isara'ila Haaretz ta rawaito cewa mambobin majalisar yaƙin Benny Gantz da Gadi Eizenk da Ministan Tsaro Yoav Gallant sun gana da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su kafin a fara taron, amma Netanyahu bai ba da amsa ba ga buƙatar mutanen ta ganawa da shi.

Isra'ilawa sun buaci Firaminista Benjamin Netanyahu ya sauka daga muƙaminsa sanna ya gudanar da sabon zaɓe. / Photo: AFP
TRT World