Dole ne Isra'ila ta ba da damar kai agaji ga Falasdinawa 'ba tare da ɓata lokaci ba' — Biden / Hoto: AFP

1522 GMT — Dole ne Isra'ila ta ba da damar kai agaji ga Falasdinawa 'ba tare da ɓata lokaci ba' — Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya buƙaci a ba da izinin kai sabbin kayan agajin gaggawa ga Falasdinawa a Gaza a daidai lokacin da babbar ƙawar Amurkan, wato Isra'ila ke fafatawa da Hamas a can.

"Za mu tabbatar da cewa an samu kayan agaji ciki har da abinci da magunguna da ruwa mai tsafta, an kuma shiga da su," in ji Biden bayan sanya hannu kan takardar kudirin samar da tallafin soji ga Isra'ila da Ukraine, wanda ya hada da dala biliyan daya na taimakon agaji zuwa Gaza.

Ya ce dole ne Isra'ila ta tabbatar da cewa duk wannan taimako ya isa ga Falasdinawa a Gaza ba tare da ɓata lokaci ba.

1323 GMT — Bai kamata a ƙyale ƙoƙarin Isra'ila na ɓoye zaluncin da take yi a Gaza ba — Erdogan

Bai kamata a ƙyale ƙoƙarin da Isra'ila ke yi na ɓoye zalunci da kisan ƙare dangin da take yi a Gaza ba, in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, a wajen wani taron manema labarai a Ankara, babban birnin ƙasar.

Domin tsawaita zamaninsa a siyasance, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana yin illa ba ga tsaron lafiyar 'yan kasarsa ba kawai, har ma da yankin, in ji Erdogan.

Ya ƙara da cewa, Turkiyya za ta ci gaba da ƙarfafa ƙoƙarinta na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, da kuma tabbatar da kai agajin jinƙai ba tare da katsewa ba.

11300 GMT — Yahudawa ƴan kama-wuri-zauna fiye da 700 ne suka mamaye Masallacin Ƙudus don wani bikin addininsu

Ɗaruruwan Yahudawa ƴan kama wuri zauna ne suka dirar wa Masallacin Ƙudus a ranar Laraba don yin taron bikin Yahudawa wato Jewish Passover.

A wata sanarwa da ta fitar, wata hukumar Harkokin Addinin Musulunci a Birnin Ƙudus ta ce Yahudawa ƴan-kama-wuri-zauna 703 ne suka shiga masallacin ƙarƙashin kariyar dakafrun Isra'ila.

Bikin addinin Yahudanci na Passover, wanda ke tunawa da hijirar Isra’ilawa daga Masar a zamanin Annabi Musa, ana ɗaukarsa a ɗaya daga cikin muhimman bukukuwa a kalandar addinin Yahudawa.

Dakarun Isra'ila sun sanya dokar hana Falasɗinawa zirga-zirga a cikin harabar Masallacin Ƙudus a yayin da ƴan-kama-wuri-zaunan ke kai kawonsu a harabar masallacin, in ji sanarwar.

Shaidu sun gaya wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an jibge dakarun Isra'ila da dama a cikin masallacin don bai wa Yahudawa ƴan-kama-wuri-zaunan kariya, waɗanda suka dinga shiga masallacin rukuni-rukuni ta wajen Ƙofar Mugharbah da ke yammacin masallacin mai tsarki.

0700 GMT — Isra'ila ta kai munanan hare-hare ta sama a sansanin Nuseirat da Rafah

Bugu-da-ƙari, jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a yankuna da dama da ke Gaza.

Falasɗinawa aƙalla uku sun mutu sannan wani mutum ɗaya ya jikkata sakamakon wani hari ta sama da dakarun Isra'ila suka kai tsakiyar Gaza.

Wata majiyar asibitin ta shaida wa Anadolu Agency cewa jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari ne a kan wani rukunin mutanea makarantar Al Arban da ke sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat, inda mutanen uku suka mutu. An kai gawawwakin mutanen asibitin Al Awda da ke cikin sansanin.

Kazalika jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a arewa maso yammacin sansanin ƴan gudun hijirar, a cewar kamfanin dillancin Falasɗinawa na Wafa.

Ranar Laraba, majiyoyi daga asibiti da jami'an tsaro a Gaza sun bayar da rahotannin da ke cewa jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a Rafah da kuma sansanin Nuseirat.

Bugu-da-ƙari, jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a yankuna da dama da ke Gaza.

0200 GMT — Majalisar Dattawan Amurka ta ba da tallafin dala biliyan 26.6 ga Isra'ila

Majalisar Dattawan Amurka ta amince a bai wa Isra’ila tallafin soji har na dala biliyan 26.6, ga ƙawar tata da ake zargi da yi wa Falasɗinawan da ke Gaza kisan ƙare-dangi ta hanyar amfani da makaman Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alƙawarin sanya hannu cikin sauri kan ƙudurin na dala biliyan 61 - wanda ya hada da tallafi ga Ukraine da Taiwan - bayan da Majalisar ta ba da amincewarta ta karshe, yana mai cewa za a fara isar da tallafin da ake buƙata a wannan makon.

Amurka ta bayyana goyon bayanta ga Isra'ila tun farkon yaƙin a watan Oktoban bara. Amurka ba ta taɓa ja da baya ba wajen bai wa Isra'ila makamai, ba tare da la'akari da asarar rayukan fararen hula da ake yi a Gaza ba.

Amurka tana bai wa Isra'ila dala biliyan 3.8 a matsayin tallafin soji na shekara-shekara kuma galibi tana bai wa ƙawayenta garkuwa a Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar Dattawan Amurka ta ba da tallafin dala biliyan 26.6 ga Isra'ila / Hoto: AP

2145 GMT — Isra'ila na shirin mamaye Rafah nan ba da jimawa ba - Rahoto

Bayan yi watsi da roƙon da ƙasashen duniya suka yi wa Isra'ila da zargin kisan ƙare-dangi da ake mata, sojojin Isra'ila na shirin mamaye birnin Rafah da ke kudancin Gaza "nan ba da jimawa ba," a cewar kafafen yada labaran Isra'ila.

A cewar kafar watsa labaran Isra'ila ta KAN, wacce ta ambato wasu majiyoyin soji da ba ta bayyana sunansu ba, rundunar sojin na shirin kai hare-hare ta ƙasa a Rafah, ciki har da "kwashe wasu mazauna yankin masu yawa."

"Bisa shirin da sojojin suka yi, za a bukaci Falasdinawa sama da miliyan daya da ke Rafah da su ƙaurace wa yankin zuwa matsugunan da aka kafa kwanan nan a yankunan kudanci da tsakiyar Zirin Gaza," a cewar kafar watsa labaran.

TRT Afrika da abokan hulda