Firaministan Indiya Modi ya jajanta sakamakon wannan gobara. / Hoto: Reuters

Jarirai shida sabbin haihuwa sun rasu sakamakon wata gobara da ta faru a wani asibitin yara a babban birnin Indiya, kamar yadda 'yan sanda a ƙasar suka tabbatar.

Firaministan Indiya Narendra Modi ya jajanta sakamakon irin ɓarnar da wannan gobara ta yi.

A lokacin gobarar wadda ta faru a asibitin da ke Delhi, mutane sun rinƙa kutsawa a cikin wutar mai ci bal-bal domin ceto yara, kamar yadda 'yan sandan suka ƙara da cewa.

Rahotanni sun ce ba a kira masu kashe gobara ba sai da wutar ta kusan cinye asibitin a ranar Asabar da dare.

Sai dai a cikin mintuna na farko bayan wutar ta tashi, waɗanda ke kusa ne suka hango gobarar kuma suka jajirce wajen ceto jariran.

A wata sanarwa da babban jami’in ‘yan sanda Surendra Choudhary ya fitar, ya ce, an ceto dukkan jariran 12 da aka haifa daga asibiti tare da taimakon wasu mutane, amma ya kara da zuwa lokacin da aka soma duba lafiyarsu, shida sun rasu.

Gobarar da ta tashi a asibitin ta tashi ne sa’o’i bayan wata gobara ta daban ta faru a wani wurin wasan yara da ke jihar Gujarat da ke yammacin Indiya wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 27 ciki har da yara hudu.

Ana yawan samun gobara a Indiya sakamakon rashin bin ƙa'idojin gine-gine da kuma yawan jama'a da rashin bin dokokin kiyaye kai.

AFP