Isra'ila ta ci gaba da kashe mutane a Gaza a kullum waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: AA

1647 GMT –– An dakatar da rabon abinci a Rafah saboda rashin tsaro –– UNRWA

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNRWA ta ce an dakatar da rabon abinci a kudacin Rafah saboda rashin tsaro da kuma ƙarancin abincin.

UNRWA ɗin ta bayyana haka a wata sanarwar da ta fitar a shafin X inda ta ce cikin cibiyoyinta 24, guda shida ne kaɗai ke aiki kuma su ma ba su samu wasu kayayyakin kiwon lafiya ba fiye da kwana 10 sakamakon rufe iyakar Rafah da Karem Shalom zuwa cikin Gaza.

Hare-haren da Isra'ila ta kai lokaci guda a yankunan kudanci da arewacin Gaza a wannan watan ya haifar da wani sabon kaura na dubban daruruwan jama'a daga gidajensu, tare da takaita zirga-zirgar kayan agaji, lamarin da ke kara fuskantar barazanar yunwa.

1337 GMT –– Oman ta yi maraba da matakin ICC kan Isra'ila

Ƙasar Oman a ranar Talata ta yi maraba da matakin da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta ɗauka na ba da sammacin kama Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan zargin aikata laifukan yaƙi.

“Ina maraba da wannan bayyanannen hukuncin na Kotun ICC,” kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Oman Badr Albusaidi ya bayyana a shafinsa na X.

“Tarihi zai tuna da masu laifi na ainahi waɗanda suke aikata kisan kiyashi da laifukan yaƙi ga bil’adama. Dole a yi adalci,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

1045 GMT –– China ta ce tana fata Kotun ICC za ta yi adalci a shari'ar Isra'ila da Gaza

China ta ce tana fata Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC za ta yi adalci bayan mai shigar da ƙara ya buƙaci a bayar da takardar sammaci ga shugabannin Isra'ila da Hamas, daga ciki har da Benjamin Netanyahu.

Ko da aka tambayi China a ranar Talata kan wannan matakin, sai Beijing ɗin ta ce "wata gagarumar yarjejeniya a tsakanin kasashen duniya sun buƙaci a gaggauta dakatar da yakin Gaza da kuma kawo karshen matsalar jin kai na al'ummar Falasdinu."

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya ce "Ana fatan kotun ta ICC za ta tabbatar da matsayinta na rashin son kai da kuma yin amfani da karfinta kamar yadda doka ta tanada."

AA
AFP
Reuters
AP