Atrash ya danganta bazuwar macizai da kunamu da zafin hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke kai wa yankin. / Hoto: AA

0120 GMT — Tsananin zafi da yaƙi sun sa macizai da kunamu na fitowa a sansanonin ‘yan gudun hijira na Gaza

‘Yan gudun hijira da ke samun mafaka a sansanonin da ke faɗin yankin Zirin Gaza sun koka kan yadda ake samun yawaiitar macizai da kunamu, saboda tsananin zafi da bala’in yaƙi da ke fito da su.

Wani mutum mai shekara 27 Mahmoud al Masry wanda ke zaune a sansanin Khan Younis, ya wallafa hoton wani maciji da aka kashe a shafinsa na Instagram ranar 27 ga watan Yuni.

“Mun asamu wanan macijin a cikin tanti da daddare. Ba don Allah ya so mu ba da tuni wani zancen ake ba wannan ba.” Kamar yadda ya rubuta a shafin nasa na IG.

Ƙaninsa ne ya ga macijin a lokacin da iyalan gidan ke zaune suna cin abincin dare, amma sun samu nasarar kashe shi da gatari.

Tsakanin Afrilu da Yuni, yayin da yanayin zafi yakan kai sama da digiri 100 a ma’aunin salshiyas a Gaza, a irin wadannan lokutan, ganin maciji da kunamu kan zama ruwan dare," in ji Imad Atrash, babban darektan kungiyar namun daji ta Falasdinu a Yammacin Kogin Jordan.

“Muna da kusan kwanaki goma na yanayin sanyi, wanda shi ne lokacin da suke yin ƙwai. Amma lokacin da yanayin zafi ya zo, macizai suna son zuwa wuraren ruwa don jin sanyi ".

“Su kuwa kunamu ba sa bukatar ruwa, amma suna bukatar inuwa. Su ƙanana ne kuma suna ɓuya a cikin duwatsu, don haka dole ne a yanzu suna ɓoye cikin ɓaraguzan gine-gine,” in ji shi.

Atrash ya danganta bazuwar macizai da kunamu da zafin hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke kai wa yankin.

"Dabbobin kuma suna kokarin tsira ne kawai," in ji shi.

“Bama-bamai sun gurbata kasar wajen. Kuna iya gani a cikin hotuna, ƙasar ta ƙone ta koma baƙa. Ba wurin zama mai dadi ga kunamu ko macizai a yanzu. Yakin ya shafi dukkan halittu masu rai, dukkan wani abu mai rai na kan tudu da na duwatsu”.

Daga cikin nau'in macizai goma zuwa goma sha biyu da aka gani a Gaza, guda biyu ne kawai aka san cewa suna dafi: wato Viper Palestine (Deborah palestinae) da kuma maciji mai launi da zane a jikinsa (Echis coloratus).

1013 GMT — Isra'ila na yin luguden wuta a Birnin Gaza yayin da masu shiga tsakani ke neman a tsagaita wuta

Mazauna Birnin Gaza sun maƙale a gidajensu sannan an kasa kwashe gawawwakin mutanen da aka kashe sakamakon luguden wutar da Isra'ila ta ƙaddamar a yankin, a yayin da Washington ke matsa lamba kan a tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a wajen tattaunawa da ake yi a Masar da Qatar.

Hamas ta ce luguden wutar da Isra'ila take yi a Birnin Gaza City a wannan makon yana iya wargaza yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin.

0441 GMT — Umarnin da Isra'ila ta bai wa Falasɗinawa su fice daga Birnin Gaza 'hauka ne zalla'

Cibiyar bayar da bayanai kan hakkokin ɗan'adam ta Yankunan da Isra'ila ta mamaye, B’Tselem, ta bayyana umarnin da sojojin Isra'ila suka bai wa dukkan Falasɗinawa na ficewa daga Birnin Gaza a matsayin “hauka zalla.”

A wani saƙo da ta wallafa a soshiyal midiya, cibiyar ta yi kira ga ƙasashen duniya su tsoma baki sannan su "nemi Isra'ila ta daina yaƙi nan-take”.

“Bisa ayyukan da Isra'ila take yi, da alama tana da niyyar ci gaba da yaƙi babu ƙaƙƙautawa, inda take lalata gine-gine da kashe mutane ba tare da sanin lokacin da za ta daina ba," in ji saƙon da ƙungiyar ta fitar.

Bisa ayyukan da Isra'ila take yi, da alama tana da niyyar ci gaba da yaƙi babu ƙaƙƙautawa, in ji cibiyar./Hoto: AA

0117 GMT — Amurka tana 'taka-tsantsan' a kan tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

Amurka tana 'taka-tsantsan' a kan tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, a cewar kakakin Fadar White House kan sha'anin tsaro John Kirby a hira da CNN.

"Muna yin taka-tsantsan game da yadda lamura ke tafiya," in ji Kirby yayin da aka tambaye shi a kan ko tattaunawar tsagaita ta zo ƙarshe.

"Har yanzu akwai babban saɓani tsakanin ɓangarorin biyu. Mun yi amannar cewa za a samu daidaito a kan wannan saɓani, kuma wannan shi ne abin da Brett McGurk da Daraktan CIA Bill Burns suƙe yunƙurin yi a halin yanzu," a cewarsa.

2212 GMT — Erdogan ya gana da Scholz a kan yaƙin Gaza

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz sun tattauna game da yaƙin da Isra'ila take yi a yankin Gaza da ta mamaye.

Erdogan ya shaida wa Scholz cewa dole ne a matsa lamba kan Isra'ila domin ta kawo ƙarshen hare-haren da take kai wa Gaza sannan kada a ɓarar da damar tsagaita wuta, a cewar Daraktan Sadarwa na Turkiyya.

Ya ƙara da cewa yana da matuƙar muhimmanci a ƙara ƙaimi wajen hana yaƙin watsuwa zuwa sauran sassan yankin.

TRT Afrika da abokan hulda