Ci gaban da aka samu na zuwa ne bayan shafe tsawon shekaru 30 da sanya hannu kan yarjejeniyar Oslo ta farko a shekarar 1993. / Hoto: Reuters   / Photo: Reuters Archive

Ƙasashen Norway da Ireland da kuma Sifaniya sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa a wani mataki mai cike da tarihi wanda ya janyo tofin Allah tsine daga Isra'ila da kuma farin-ciki daga Falasɗinawa.

Tuni dai Isra'ila ta ba da umarni ga jakadunta da ke ƙasar Norway da Ireland su koma gida.

Sanarwar ta ranar Laraba ta zo ne cikin tsantsar farin-ciki, inda Firaministan Norway Jonas Gahr Store ya fara bayyana matsayar ƙasarsa yana mai cewa "ba za a taɓa samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ba idan ba a tabbatar da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba."

Gahr Store ya ce ƙasarsa za ta amince da ƙasar Falasdinu a hukumance daga ranar 28 ga watan Mayu.

"Ta hanyar amincewa da ƙasar Falasɗinu, Norway na goyon bayan shirin zaman lafiyar Larabawa," in ji shi.

A makonnin da suka gabata ne dai ƙasashen ƙungiyar Tarayyar Turai da dama suka bayyana shirinsu na amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa, suna masu kafa hujja da cewa zaman lafiya ba zai samu ba a Gabas ta Tsakiya sai an samar da ƙasashe biyu.

Norway, wacce ba mamba ba ce a ƙungiyar Tarayyar Turai, amma a koyaushe tana kan bakanta na nuna matuƙar goyon bayan samar da ƙasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.

"Falasɗinu tana da 'yancin samun damar zama ƙasa mai cin gashin kanta," a cewar shugaban gwamnatin Norway.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila suka kai hare-hare a yankunan arewanci da kudancin Gaza a cikin wannan wata na Mayu, lamarin da ya haifar da wani sabon yanayi na gudan hijira na dubun- dubatan mutane tare da takaita shigowar kayan agaji, yanayin da ke kara ta'azzara barazanar yunwa da ake fuskanta.

Don haka daga yanzu ''kasar Scandinavia za ta dauki Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta tare da dukkan hakkoki da wajibai da suka rataya a wuyanta," in ji Gahr Store.

Ci gaban da aka samu na zuwa ne bayan shafe tsawon shekaru 30 da sanya hannu kan yarjejeniyar Oslo ta farko a shekarar 1993.

Tun daga wancan lokacin, "Falasɗinawa suka ɗauki matakai masu muhimmanci wajen samar da ƙasashe biyu," in ji gwamnatin Norway.

Ya ƙara da cewa Bankin Duniya ya yanke shawarar cewa Falasɗinu ta cika muhimman sharuɗɗa don yin aiki a matsayin ƙasa a shekara ta 2011, kana an gina cibiyoyin ƙasa da ƙasa don samar wa jama'a muhimman ayyuka.

"Yakin Gaza da kuma ci gaba da fadada haramtattun matsugunan a yankin Yammacin Kogin Jordan har yanzu hakan na nufin cewa halin da Falasdinu ke ciki ya kara tsanani fiye da shekaru da dama da suka wuce," in ji gwamnatin Norway.

'Ranar tarihi da muhimmanci'

Kazalika a ranar Laraban ne, Firaministan Ireland Simon Harris ya fitar da sanarwar ƙasarsa kan amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa, yana mai cewa wani mataki ne na haɗin-gwiwa da ƙasar Sifaniya da kuma Norway. "Rana ce mai tarihi da muhimmanci ga Ireland da Falasɗinu," in ji shi.

Harris ya ce an ɗauki matakin ne da nufin sasanta rikicin Isra'ila da Falasɗinu ta hanyar samar da ƙasashe biyu.

Firaministan Ireland ya ce yana ganin sauran ƙasashe za su bi matakin Norway da Sifaniya da kuma Ireland wajen amincewa da ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken iko ''a cikin makonin masu zuwa.''

Firaministan Sifaniya Pedro Sanchez ya ce ƙasarsa za ta amince da ƙasar Falasɗinu a ranar 28 ga Mayu.

Sanchez, shugaban ƙasar Sifaniya tun daga shekarar 2018, ya fitar da wannan sanarwar ne da ake ta sa rai a kai wa majalisar dokokin ƙasar a ranar Laraba.

Firaministan Sifaniya dai ya shafe watanni da dama yana rangadin ƙasashen Turai da Gabas ta Tsakiya domin samun goyon bayan amincewa da ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yancin kanta da kuma yiwuwar tsagaita wuta a Gaza.

A farkon wannan watan nan ne Ministan Harkokin wajen Sifaniya Jose Albares ya ce ya sanar da Sakataren Harkokin wajen Amurka Antony Blinken aniyar gwamnatinsa ta amincewa da ƙasar Falasɗinu.

TRT World