Ana sa ran yarjejeniyar ta shekaru 10 za ta "matukar"  karfafa kokarin gwamnatin Somaliya na kare ikonta. / Hoto: Taskar AA      

Wani jirgin ruwan Turkiyya ya isa tashar jiragen ruwa ta Mogadishu bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da tattalin arziki tsakanin Somaliya da Turkiyya a watan Fabrairun bana.

A ranar Talata ne jirgin Kinaliada F514 ya isa tashar jiragen ruwan, watanni biyu bayan wata muhimmiyar yarjejeniya da ƙasashen biyu suka rattabawa hannu, wadda a ƙarƙashinta Turkiyya ta amince da bayar da tallafin tsaron teku ga Somaliya.

Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da ministocin ƙasar da dama da kuma jakadan Turkiyya a Somaliya, Alper Aktas, sun halarci bikin tarbar jirgin.

Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaba Mohamud ya yaba wa Turkiyya bisa taimakon da take bai wa Somaliya, inda ya kira ta da matsayin "ƙawarmu kuma 'yan'uwarmu".

Ya gode wa Ankara bisa ga yarjejeniyar tsaron, inda ya ƙara da cewa a yanzu sojojin ruwan Somaliya za su ƙara samun ƙarfin gwiwa.

Ministan tsaron Somaliya Abdulkadir Mohamed Nur ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa yarjejeniyar ta bayyana alaƙa mai ƙarfi da ke tsakanin ƙasashen biyu.

'Tarihin' yarjejeniyar

Ministocin tsaron Turkiyya da na Somaliya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin-gwiwa a watan Fabrairu domin inganta alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu da kuma zaman lafiyar yankin.

Yarjejeniyar ta shekaru10 ce wadda za ta yi "matuƙar" ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin Somaliya na kare 'yancinta, a cewar ministan yaɗa labaran kasar Daud Aweis bayan da majalisar dokokin ƙasar ta amince da yarjejeniyar.

Kazalika, Firaiminista Hamza Abdi Barre ya yaba da yarjejeniyar a matsayin "mai cike da tarihi," yana mai gode wa gwamnatin Turkiyya da al'ummarta saboda ci gaba da goyon bayan da suke bai wa gwamnati da al'ummar yankin Kusurwar Afirka.

Ofishin jakadancin Ankara mafi girma a Afirka na Mogadishu, sannan ta gina cibiyar soji mafi girma a ƙetare a can don horar da sojojin ƙasar Somaliya.

TRT World