WASANNI
2 minti karatu
Kocin Man United ya mayar wa Ronaldo martani kan sukar halin da kungiyar ke ciki
Kocin Manchester United, Ruben Amorim ya mayar da martani ga tsohon ɗan wasan ƙungiyar Cristiano Ronaldo gabanin wasansu da Tottenham a ranar Juma'a.
Kocin Man United ya mayar wa Ronaldo martani kan sukar halin da kungiyar ke ciki
Kamar Cristiano Ronaldo, shi ma Ruben Amorim ɗan asalin Portugal ne.
4 awanni baya

Kocin Manchester United, Ruben Amorim ya nemi ƙungiyarsa da masoyanta su kalli gaba, su daina tunawa da munanan kurakuran da ƙungiyar ta samu kanta ciki a baya.

Kocin na magane ne kan kalaman da tsohon tauraron ƙungiyar, Cristiano Ronaldo ya yi, inda ya koka kan yanayin da tawagar United take ciki tsawon lokaci har zuwa yau.

Da yake amsa cewa an tafka kurarakurai a zamaninsa da zamanin tsaffin kociyoyin ƙungiyar, Amorim ya sha alwashin kawar da manyan matsalolin da ke damun ƙungiyar.

A kwanakin nan ne Ronaldo ya yi wata hira da sanannen ɗan-jaridan Burtaniya, Piers Morgan, inda ya taɓo batutuwa ciki har da matsalar da United ke ciki na rashin tagomashi.

Ronaldo ya nuna takaicinsa kan rugujewar kimar United, duk da ya amsa cewa yana ƙaunar ƙungiyar har zuwa yanzu.

Ba buƙatar ‘tsafi’

Cristiano Ronaldo ya ƙara da cewa kocin yanzu na Manchester United, Ruben Amorim ba zai iya amfani da wani ‘tsafi’ don warkar da ƙungiyar ba.

A Nuwamban nan Ronaldo ya cika shekaru uku da barin United, kuma Amorim ba ya cikin kociyoyin da suka horar da shi a duka lokuta biyu da ya taka wa ƙungiyar leda.

Sai dai a martanin nasa, Amorim ya ce, "Tabbas (Ronaldo) yana da tasiri kan duk abin da ya faɗa.

Ya kuma ƙara da cewa, “Abin da muke buƙata shi ne mu kalli gaba. Mun san mun yi kurakurai a baya, amma muna ƙoƙarin kawo sauyi”.