Rundunar hadakar soji da Saudiyya ke jagoranta ta kai wasu munanan hare-hare kan 'yan awaren Majalisar Wucin Gadi ta Kudancin kasar (STC) da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ke mara wa baya a Yemen, inda suka kashe akalla mutum bakwai.
Mohammed Abdulmalik, shugaban rundunar STC a Wadi Hadramaut da Hamadar Hadramaut, ya ce hare-haren sama guda bakwai sun afka wa sansanin Al-Khasah, inda suka kashe mutum bakwai tare da raunata fiye da 20.
Ya ƙara da cewa ƙarin hare-hare sun fada kan wasu wurare a wannan yanki.
Mace-macen su ne na farko da aka samu ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta soji da Saudiyya ke jagoranta tun lokacin da STC ta kwace yankunan lardunan Hadramaut da Mahra a watan da ya gabata
Gwamnan Hadramaut Salem al-Khanbashi ya ce an kai hare-haren saman ne da nufin samun dakarun da suka kai hari kan sassan “Dera Al-Watan” yayin da suke kutsawa don ƙwace iko da sansanonin soji.
Ya kuma yi kira ga mazauna Hadramaut da su guji tsoma baki ga rundunonin ko kwanton ɓauna yayin da ake tura su bakin aiki.
Khanbashi ya sanar da kai harin ne jim kadan bayan naɗa shi ya jagoranci rundunar 'National Shield' da Saudiyya ke tallafawa a wannan lardi mai arzikin albarkatun ƙasa da ke kan iyakar Saudiyya.
STC ta ce tun da fari an saka dakarunta cikin shirin ko-ta-kwana bayan da gamayyar soji da Saudiyya ke jagoranta, wadda aka amince da ita a duniya, ta sanar da kai harin don ƙato sansanonin soji a lardin.
Tura jiragen ruwa a Tekun Larabawa
A halin yanzu, Rundunar Sojin Ruwa ta Masarautar Saudiyya ta tura jirage a Tekun Larabawa don fara ayyukan bincike da yaki da fataucin kayayyaki, in ji mai magana da yawun kawancen soji na Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya.
Turki al-Maliki a shafin X ya ce tura jiragen ruwa yana nufin karfafa sa ido a teku da aiwatar da ayyukan samame domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.
Haka kuma a ranar Jumma'a, jakadan Saudiyya a Yemen, Mohammed Al Jabir ya ce STC ta hana wata tawaga daga Riyadh sauka a filin jirgin Aden, inda ya zargi kungiyar da 'rashin sassauci'.
Saudiyya 'ta sha fuskantar ƙin amincewa da rashin sassauci daga shugaban (SCT) Aidaros Alzubidi, a kwanan nan kan ƙin bayar da izinin jirgi da ke ɗaukar tawagar jami'an Saudiyya', Al Jabir ya wallafa a X.















