A Jamhuriyar Nijar shirin wayar da kan jama’a na shekarar 2025 kan iya karatu ya kai ga mutum 24,573, ciki har da mata 19,619, inda aka gwada mutum 18,741 a cikinsu kuma aka tabbatar da cewa mutum 13,132 sun iya karatu, wato kashi 70.07 cikin 100 ke nan.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ANP ya ruwaito cewa Ministar Ilimin ƙasar Dakta Élisabeth Shérif ce ta bayyana hakan ranar Lahadi a jawabin da ta yi albarkacin Ranar Iya Karatu ta Duniya.
Dakta Elisabeth Shérif ta ce wannan sakamakon ya samu ne sakamakon matakan da shugabannin Nijar suka ɗauka waɗanda suka kamata a yabawa.
Ta ce bisa ga nauyin da Shugaban ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ya ɗora mata, "an yi muhimman gyare-gyare kuma duk da ƙalubale iri-iri da ke fuskantar ƙasarmu, ana ci gaba da ƙara kasafin kuɗin da ake ware wa wannan batu domin amfani da iya karatu da shirin ilimin yaƙi da jahilci wajen magance matsalolin ɓangarori daban daban wajen samar da al’umma mai ƙarin adalci da ilimi da za ta iya tunkarar ƙalubalen ci-gaba."
Ministar wadda ke kula da iya karatu ta ce jajircewar da shugabannin Nijar ta ba da ikon ƙaddamar da sabbin shirye-shirye na ruɓanya adadin waɗanda suka iya karatu da kuma amfani da harsunan cikin ƙasar a matsayin hanyoyin koyarwa.
Ta bayyana cewa Nijar "ta riga ta fara shigar fasahar komfuta cikin koyar da karatu da kuma shirin yaƙi da jahilci .”
Ta kuma bayyana cewa za a fara shirin “ilimi ta salula” tsakanin shekarar 2025 zuwa shekarar 2026 a wasu yankunan ƙasar.