| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Daesh na amfani jirage marasa matuƙa da hanyoyin kimiyya don aikata ta'addanci a Nijeriya - Rahoto
Rahoton, wanda aka wallafa a ranar Alhamis, ya ce ’yanta’addan sun mayar da fasahohin da ake amfani da su a harkokin kasuwanci da na yau da kullum zuwa kayan aikin tattara bayanan sirri da yaɗa farfaganda da gudanar da hare-hare.
Daesh na amfani jirage marasa matuƙa da hanyoyin kimiyya don aikata ta'addanci a Nijeriya - Rahoto
Nijeriya na fama da matsalar ta’addanci tun daga shekarar 2009, inda ƙungiyoyin ’yan ta’adda ke ƙara rungumar sabbin fasahohi domin ƙarfafa ayyukansu. / Others
 

’Yanta’addan Daesh a Nijeriya na ƙara amfani da jiragen sama marasa matuƙa masu ɗauke da makamai da hanyoyin sadarwar tauraron ɗan’adam da kuma hanyoyin samun kuɗaɗe daga ƙasashen duniya domin ci gaba da ayyukan ta’addancinsu, a cewar wani sabon rahoto da Cibiyar Nazarin Tsaro (ISS) ta fitar.

Rahoton, wanda aka wallafa a ranar Alhamis, kuma Taiwo Adebayo ya rubuta, ya ce ’yanta’addan sun mayar da fasahohin da ake amfani da su a harkokin kasuwanci da na yau da kullum zuwa kayan aikin tattara bayanan sirri da yaɗa farfaganda da gudanar da hare-hare.

Nijeriya na fama da matsalar ta’addanci tun daga shekarar 2009, inda ƙungiyoyin ’yan ta’adda ke ƙara rungumar sabbin fasahohi domin ƙarfafa ayyukansu.

Binciken na ISS ya dogara ne kan hirarraki da mutane 17 masu muhimmanci, ciki har da tsoffin ’yanta’adda, jami’an tsaro da leƙen asiri, fararen-hula da masu bincike. An gudanar da hirarrakin ne tsakanin watan Afrilu da Satumba na shekarar 2026.

Sakamakon binciken ya yi daidai da wani rahoto da aka fitar a watan Yuli, wanda ya ce ’yanta’addan Nijeriya sun mayar da amfani da fasahar AI wani ɓangare na ayyukansu, inda suke amfani da ita wajen tsara dabarun yaƙi da ƙera bama-bamai, da sauran ayyuka.

A cewar rahoton na ISS, ƙungiyar Daesh ta wuce amfani da jiragen sama marasa matuƙi wajen sa ido kawai, inda yanzu take sanya abubuwan fashewa da aka ƙera cikin sauƙi a kan jiragen da ake sayarwa a kasuwa.

Rahoton ya ce an yi amfani da irin waɗannan jirage wajen kai hare-hare akai-akai kan sansanonin sojoji a arewa maso gabashin Nijeriya.

Rahoton ya kuma bayyana cewa ƙungiyar na cin gajiyar alaƙarta da shugabannin cibiyar sadarwar Daesh ta duniya, waɗanda ke samar mata da horon ta ɓangaren fasaha, kuɗaɗe da kayayyakin yaɗa labarai.

Wannan na ba ta damar samun galaba kan sauran ƙungiyoyin ’yanta’adda da ke hamayya da ita.

Binciken ya gano cewa akwai wuraren da suke samun kayayyaki da suka haɗa da Legas, Kano da Dubai, da kuma masu harkar canjin kuɗi da ke taimakawa wajen biyan kuɗaɗe da sayen kayan aiki.

Rahoton ya ce: “Sau da yawa waɗannan hanyoyin suna cuɗanya da harkokin kasuwanci na halal, lamarin da ke sa gwamnati ta fuskanci ƙalubale wajen ware su da kuma kai musu hari.”