| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ghana za ta nemi shiga ƙungiyar BRICS
Ghana ta bayyana cewa shiga wannan ƙungiya zai karfafa dangantakar da take da ita da abokan hulɗar ci gabanta a baya maimakon maye gurbinsu.
Ghana za ta nemi shiga ƙungiyar BRICS
Ghana na son zama mamba a ƙungiyar BRICS

Ghana za ta gabatar da bukatar shiga ƙungiyar BRICS a hukumance bayan majalisar ministocin Shugaba John Dramani Mahama ta amince da matakin, a cewar Ministan Harkokin Waje, Samuel Okudzeto Ablakwa.

Kamfanin Dillancin Labaran Ghana ya rawaito Ablakwa na cewa, wannan mataki na daga cikin kokarin fadada huldar kasa da kasa ta Ghana da kuma samar da karin damammaki na ci gaban tattalin arziki.

"Wani muhimmin batu da nake son bayyana wa al'ummar Ghana a karon farko shi ne cewa, majalisar ministocin Shugaba John Dramani Mahama ta yanke shawarar cewa ya kamata Ghana ta gabatar da bukatar shiga ƙungiyar BRICS a hukumance," in ji Ablakwa a ranar Talata.

Ministan ya ce shiga ƙungiyar zai karfafa dangantakar da Ghana ke da ita da abokan hulɗar ci gabanta maimakon maye gurbinsu.

“Kun san cewa mu mambobi ne na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya, kuma mu ne muka kafa cibiyoyin hada-hadar kuɗi na haɗin gwiwa na ƙasashen Afirka.

“Amma ƙungiyar BRICS za ta ba mu damar samun zabin hanyoyin ci gaba, kuma yana da kyau a samu zabin hanyoyi daban-daban,” in ji shi.

Haɗin gwiwa iri dabn-daban

Ablakwa ya bayyana cewa wannan matakin ya yi daidai da manufar gwamnatin Mahama ta mayar da Ghana daga matakin daidaita tattalin arziki zuwa matakin samun ci gaba mai cike da sauyi.

Ya ambaci ƙasashen Indiya da Brazil da kuma China a matsayin muhimman abokan hulɗar tattalin arziki, tare da jaddada karuwar cinikayya tsakanin Ghana da Indiya. Ya ce cinikayyar bangarorin biyu ta ninka fiye da sau biyu, inda ta tashi daga dala biliyan 3 zuwa kusan dala biliyan 7.

Ablakwa ya ce gwamnati na shirya takardar neman zama mamba a hukumance kuma za ta nemi goyon bayan ƙasashen da tuni suke cikin ƙungiyar ta BRICS.

Ya kara da cewa Ghana ta nemi goyon bayan Indiya a hukumance game da batun neman shiga kungiyar, kuma ta samu amsa ta karfafa gwiwa daga Subrahmanyam Jaishankar, Ministan Harkokin Wajen Indiya, wanda ke ziyarar aiki a Accra.

Menene BRICS?

An kafa ƙungiyar ne da sunan BRIC, wadda ta kunshi ƙasashen Brazil, da Rasha, da Indiya da kuma China, kuma an tabbatar da ita a hukumance a taron farko na ministocin harkokin waje na ƙasashen BRIC, wanda aka gudanar a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya a New York a shekarar 2006.

Ƙungiyar ta fadada a watan Janairun 2024 lokacin da ƙasar Masar, da Habasha, da Iran, da Saudiyya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka shiga, sannan Indonesia ta biyo baya a watan Janairun 2025.

A halin yanzu, BRICS tana da cikakkun mambobi 11 wato Brazil, China, Masar, Habasha, Indiya, Indonesia, Iran, Rasha, Saudiyya, Afirka ta Kudu da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

A shekarar 2025 ne ƙasashen Belarus, Bolivia, Kazakhstan, Cuba, Malaysia, Nijeriya, Thailand, Uganda, Uzbekistan da Vietnam suka shiga ƙungiyar a matsayin ƙasashe abokan hulda.

Kungiyar tana samar da dandamali don tattaunawa da haɗin gwiwa kan batutuwan siyasa da tattalin arziki na duniya da na yankuna, ciki har da kokarin kawo sauyi a cibiyoyin gudanarwa na ƙasa da ƙasa.