| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Fidan ya nemi Kasashen Musulmi su taimaka a tsara sabon tsarin duniya da Falasdinu a Ma’aunin Ƙa'ida
“Matakan da muka ɗauka a yau za su taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar duniyar Musulmi,” in ji shi, yana mai nuni da bullar sabbin cibiyoyin ƙarfin siyasa, tattalin arziki da fasaha, musamman a yankin Gabas.
Fidan ya nemi Kasashen Musulmi su taimaka a tsara sabon tsarin duniya da Falasdinu a Ma’aunin Ƙa'ida
Fidan ya nemi Kasashen Musulmi su taimaka a tsara sabon tsarin duniya da Falasdinu a Ma’aunin Ƙa'ida / َAA
 

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya yi kira ga ƙasashen Musulmi da su taka rawa wajen tsara sabon tsarin hulɗar ƙasa da ƙasa da ke kunno kai, yana mai bayyana Falasdinu a matsayin “muhimmin ma’aunin ɗabi’a da ƙa’ida” ga al’ummar Musulmi, tare da jaddada bukatar ɗaukar matakan haɗin gwiwa domin kai agajin jin ƙai da sake gina Gaza.

Da yake jawabi a wajen buɗe taron Al Sharq Forum na shekarar 2026 a Istanbul ranar Asabar, Fidan ya ce ƙasashen da ke wakiltar sama da kashi ɗaya bisa huɗu na al’ummar duniya suna da damar yin tasiri kan shawarwarin da tsawon shekaru da dama wasu ƙasashe ne ke yanke su.

“Matakan da muka ɗauka a yau za su taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar duniyar Musulmi,” in ji shi, yana mai nuni da bullar sabbin cibiyoyin ƙarfin siyasa, tattalin arziki da fasaha, musamman a yankin Gabas.

Fidan ya ce Turkiyya ta yi tsayin daka wajen adawa da “kisan kiyashin da ake yi a Gaza da ta’addancin Yahudawa ’yan-kama-wuri-zauna a Yammacin Kogin Jordan”.

Ya buƙaci ƙasashen Musulmi da su jagoranci ƙoƙarin kai agajin jin ƙai ga Falasɗinawa da kuma sake gina Gaza.

Ya ce hanya ɗaya tilo ta samar da zaman lafiya na gaskiya kuma mai ɗorewa ita ce aiwatar da tsarin ƙasashe biyu, wanda zai bai wa Falasɗinawa ƙasa mai cin gashin kanta, tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta.

Ya kamata ƙasashen yankin su jagoranci harkokin tsaro

Fidan ya ce ya kamata ƙasashen da ke fuskantar illolin wani mataki su kasance a sahun gaba wajen yanke shawarar da ta shafe su.

Ya kawo misalin ƙawancen tsaro da Turkiyya, Saudiyya da Pakistan suka kafa, wanda wakilan ƙasashen suka gudanar da taro a Islamabad ranar Juma’a, a matsayin wata hanya ta aiwatar da wannan manufa.

Fidan ya ce kowace ƙasa na da irin gudummawar da za ta iya bayarwa da kuma ƙwarewar da take da ita wajen ƙarfafa ƙawancen. Ya bayyana cewa yana sa ran wasu ƙasashen yankin za su shiga ƙawancen yayin da ake ci gaba da gina hukumomi da tsarin gudanar da shi.

Ya kuma yi nuni da ƙungiyar Regional Quartet, wadda ta ƙunshi Turkiyya, Masar, Pakistan da Saudiyya, domin samar da matsaya ɗaya kan rikice-rikicen yankin.

Ministan ya ce ya kamata haɗin gwiwar ƙasashen ya wuce batun tsaro, yana mai bayyana cinikayya, ƙarfafa dangantakar tattalin arziki da haɗin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha a matsayin muhimman abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kansu.

A cewar Fidan, manufar ƙarfafa haɗin gwiwar ita ce bai wa ƙasashe damar taka rawa wajen tsara yadda tsarin hulɗar ƙasa da ƙasa ke gudana.

Ya ce burin shi ne samar da tsarin duniya da ya fi wakiltar muradun ƙasashe daban-daban, wanda aka gina bisa adalci da halaccin doka.