| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta kama masu leƙen asirin intanet da ke kai hari kan muhimman hukumomin gwamnati
Hukumar leƙen asirin Turkiyya ta ce mutane biyu da ake zargi sun yi kutsen tattara bayanan hanyoyin sadarwar Wi-Fi a Ankara da Istanbul ga wata hukumar leƙen asiri a ƙasar waje, inda ake biyansu kuɗin kirifto.
Turkiyya ta kama masu leƙen asirin intanet da ke kai hari kan muhimman hukumomin gwamnati
Binciken MIT ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargin suna gudanar da ayyukan ne a madadin hukumar leƙen asirin wata ƙasa ta waje / TRT Haber
 

Hukumar Leƙen Asirin Ƙasa ta Turkiyya (MIT) ta sanar da kama wasu masu leƙen asiri ta intanet da ke kai hari kan hanyoyin sadarwar intanet na muhimman hukumomin gwamnati, ciki har da na masana'antar tsaro.

An kama mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin a wani samame a maɓoyarsu, a cewar majiyoyin tsaron ƙasar.

An gudanar da samamen ne a ranar Alhamis, ƙarƙashin haɗin gwiwar hukumar MIT da rundunar 'yansandan Istanbul, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa wasu mutane biyu na ƙoƙarin yin kutse a hanyoyin sadarwar muhimman cibiyoyin ƙasar.

Bincike ya gano cewa waɗanda ake zargin sun yi amfani da wasu manhajoji da na'urori na musamman wajen gano da tattara bayanan hanyoyin sadarwar Wi-Fi, yayin da suke bin wasu hanyoyi sadarwa da aka tsara a biranen Ankara da Istanbul, kamar yadda MIT ta bayyana.

Hukumar ta yi ta bibiyar waɗanda ake zargin inda jami'anta da 'yansandan Istanbul suka kama su a wani samame na haɗin gwiwa.

A yayin amsa tambayoyi, waɗanda ake zargin sun amince cewa suna aiki tare da kutse kan hanyoyin sadarwar muhimman cibiyoyin gwamnati da masana'antar tsaro da hedkwatar jam'iyyun siyasa da sansanonin sojoji da kuma ofisoshin jakadanci da ke Ankara.

Kazalika, sun shaida wa masu bincike cewa, suna samun umarnin gudanar da ayyukan ne ta hanyar tallace-tallacen ayyuka da ake wallafawa a shafukan sada zumunta, kuma ana biyansu lada ta hanyar kuɗaɗen intanet wato (cryptocurrency).

Ƙarin bincike ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargin suna gudanar da ayyukan ne a madadin hukumar leƙen asirin wata ƙasa ta waje, a cewar MIT.

Daga bisani, an tsare mutanen biyu a gidan yari yayin da ake jiran soma shari'arsu.