Masu shigar da ƙara a ƙasar Masar a ranar Alhamis, sun sanar da cewa sun kama wani mutum da ake zargi da haddasa wata babbar gobara da ta tashi bayan wata tankar mai ta kife a kan babbar hanyar mota mai cike da jama’a a birnin Alkahira, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 31.
Masu shigar da ƙarar sun ce mutumin ya amsa cewa yana gudu ta mota fiye da kima a lokacin da motarsa ta yi karo da tankar mai, lamarin da ya sa sitiyarin motarsa ya sulale daga hannunsa, motar kuma ta kauce daga hanyar da take bi.
A cewar masu gabatar da ƙarar, lokacin da motar ta bugi tankar, ɗaya daga cikin tayoyin motar ya fashe, wanda ya jawo kifewar tankar. Sun ƙara da cewa malalar man fetur ce ta haddasa tashin gobarar.
Hotunan bidiyo daga wurin da lamarin ya faru sun nuna yadda dunƙulen baƙin hayaƙi ke tashi sama a unguwar Al-Waraq da ke cikin birnin Alkahira mai cunkoson jama'a inda a lokacin da lamarin ya faru, direbobin motocin da ke kan babbar hanyar da ya zagaye birnin sun rinƙa latsa odar motarsu da neman hanyar tserewa.
Agajin gaggawa
Ma'aikatar Lafiya ta Masar ta ce an tura motocin ɗaukar marasa lafiya guda 39 zuwa wurin da hatsarin ya faru, inda aka kai mutane 15 asibiti sakamakon raunukan da suka samu. Hudu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
“Akwai tashin hankali a wurin,” in ji Abdel Rahman Khalil, wanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya isa wurin jim kaɗan bayan hatsarin, inda ya tarar da tankar mai a kife tana ci da wuta.
Hotunan da AFP ta ɗauka sun nuna mummunan yanayin da wurin ya kasance, inda motoci da dama suka ƙone kurmus, yayin da jami'an kashe gobara ke ci gaba da kashe wutar da ta kama ragowar tankar.
Babban mai gabatar da ƙara na Masar ya ce an ƙaddamar da bincike kan lamarin, kuma ana gudanar da gwajin ƙwayoyin halitta na DNA domin gano waɗanda gobarar ta ƙone sosai har ta sauya kamanninsu.
Ma'aikatar Lafiya ta ce ta ƙara matakin gargaɗin gaggawa, yayin da Ministan Lafiya, Khaled Abdel Ghaffar, ya ziyarci wurin da hatsarin ya faru da wasu asibitocin da ke kusa.
Hotunan da tashar Al-Qahera News ta watsa sun nuna ana kwashe ragowar tankar da gobara ta ƙone, yayin da aka fara buɗe wasu sassan hanyar domin zirga-zirgar ababen hawa ta ci gaba.
An fara bincike
Wani mai magana da yawun majalisar ministocin Masar ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na cikin gida cewa Firaminista Mostafa Madbouly ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Ya ce gwamnati na jiran cikakken bayani kan lamarin kafin yanke shawarar “matakan da za a ɗauka nan gaba game da jigilar kayayyakin man fetur da kuma tabbatar da tsaro da kariya yayin gudanar da irin waɗannan ayyukan jigilar mai”.
A cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasar Masar, kusan mutane 6,000 ne suka mutu a hatsaran ababen hawa a faɗin ƙasar a bara.
A shekarar da ta gabata kafin hakan kuma, hukumomi sun ce fiye da mutane 5,200 ne suka mutu a hatsarin mota a faɗin ƙasar.
A watan Agusta, aƙalla mutane 18, mafi yawansu matasa, sun mutu a arewacin Masar bayan haɗarin da ya haɗa da wasu motocin ɗaukar kaya guda biyu da ke ɗauke da ma'aikatan gona na wucin-gadi.
Madogara: AFP















