| Hausa
TATTALIN ARZIKI
6 minti karatu
Kasuwancin Turkiyya da ƙasashen OIC ya ƙaru yayin da tattalin arzikin Halal ke ƙara bunƙasa
Kasuwancin Turkiyya da ƙasashe 57 mambobin Ƙungiyar Haɗin Kan Musulmai (OIC) ya kai dala biliyan 136.5 a bara, yayin da ƙasar ke shirin ƙara yawan kason kasuwancin OIC cikin jimillar kasuwancinta zuwa kashi 30 cikin ɗari nan da shekarar 2028.
Kasuwancin Turkiyya da ƙasashen OIC ya ƙaru yayin da tattalin arzikin Halal ke ƙara bunƙasa
Taron Koli na Halal na Duniya karo na 12ya gudana ne a Istanbul kuma hada kamfanoni 225 daga kasashe 25. / AA
 

Kasuwancin Turkiyya da ƙasashen Ƙungiyar Haɗin Kan Musulmai (OIC) ya karu da kashi 10 cikin ɗari a cikin watanni 10 na farkon shekarar nan, inda ya kai dala biliyan 122.8.

Da yake jawabi a wajen taron koli na 12 kan kasuwanci da baje kolin kayayyakin Halal na OIC da aka gudanar a Istanbul, Ministan Kasuwanci naTurkiyya, Omer Bolat ya ce kasuwancin ƙasar da sauran ƙasashen ƙungiyar ya kai dala biliyan 136.5 a bara.

An gudanar da tarukan ne a Cibiyar Baje Kolin Istanbul, ƙarƙashin kulawar Shugaba Recep Tayyip Erdogan, tare da haɗin gwiwar Ma'aikatar Kasuwancin ƙasar. Taron ya haɗa kamfanoni 225 daga ƙasashe 25.

Bolat ya ce kason OIC cikin kayayyakin da Turkkiya ke fitarwa zuwa ƙasashen waje ya tashi daga kashi 11 cikin ɗari a shekarar 2002 zuwa kashi 27 a bana.

Ya ce burin ƙasar shi ne kai wannan kaso zuwa kashi 30 cikin ɗari na jimillar kasuwancinta kafin ƙarshen shekarar 2028.

Ya ƙara da cewa tattalin arzikin Turkiyya ya bunƙasa fiye da sau bakwai ta fuskar darajar dala tun shekarar 2002, inda ya kai dala tiriliyan 1.7, yayin da darajar kayayyakin da take fitarwa zuwa ƙasashen waje ta tashi daga dala biliyan 36 zuwa dala biliyan 285.5.

A cewarsa, ƙasashe 57 mambobin OIC suna da jimillar kuɗaɗen shiga na ƙasa da ya kai kusan dala tiriliyan 10, kuma sun samu matsakaicin bunƙasar tattalin arziki na kashi 4.1 cikin ɗari a bara, wanda ya zarce matsakaicin bunƙasar tattalin arzikin duniya na kashi 3.4.

Kasuwanci tsakanin ƙasashen OIC

Bolat ya bayyana cewa kasuwanci tsakanin ƙasashen OIC ya kai dala biliyan 979, adadin da ya wakilci kashi 19.5 cikin ɗari na jimillar kasuwancinsu da sauran ƙasashen duniya.

Ya jaddada muhimmancin tsarin fifita kasuwanci tsakanin ƙasashen OIC (TPS-OIC), wanda ke da manufar rage haraji da sauran shingayen da ke kawo cikas ga kasuwanci.

Ya ce yawan kuɗin da ake kashewa a duniya wajen sayen kayayyaki da ayyukan da suka dace da ƙa'idojin kayayyakin Halal, da suka haɗa da fanni abinci, da yawon buɗe ido, da masaku, da magunguna, da kayan kwalliya da kuma kafafen yaɗa labarai, ya kai dala tiriliyan 2.6 a shekarar 2024.

Ya ce wannan kasuwa na samun bunƙasar kashi 7 cikin ɗari a duk shekara, kuma ana hasashen za ta haura dala tiriliyan 3.5 nan da shekarar 2029.

Bolat ya bayyana cewa ɓangaren abinci ne ke da kaso mafi girma, inda ya kai dala tiriliyan 1.5, yayin da kadarorin harkokin kuɗi na Musulunci a duniya suka kai dala tiriliyan 6.

Dangane da samar da ƙa'idoji iri ɗaya, ya ce Cibiyar sa ido kan inganci da Ma'auni ta Ƙasashen Musulunci (SMIIC) ta fitar da ƙa'idoji 81, ciki har da wasu 21 da suka shafi harkokin Halal kai tsaye, a ƙasashe 49 mambobi da masu sa ido.

Kazalika ya ce Hukumar Kula da kuma Amincewa da Takardun Shaidar Halal ta Turkiyya ta amince da hukumomi 147 da ke kula da shaidar takardun Halal 3,000.

Ana sa ran baje kolin na bana zai samu baƙi aƙalla 35,000, idan aka kwatanta da 31,800 da aka samu a bara.

Masu AlakaTRT Afrika - Kungiyar OIC ta yi Allah wadai da hare-haren 'yan Houthi a Makka da yankin Madina

Tattalin arzikin Halal

Mataimakin Ministan Masana'antu da Kasuwanci na Afghanistan, Mawlawi Shahabuddin Saqeb, ya ce bai kamata a ɗauki tattalin arzikin Halal a matsayin wata kasuwar kasuwanci kawai ba, domin yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba mai ɗorewa, da ayyukan yi da kuma jawo masu zuba jari.

Ya gayyaci 'yan kasuwa da masu zuba jari daga Turkiyya da sauran ƙasashen Musulmai zuwa Afghanistan, tare da kira ga ƙasashen OIC da su daidaita ƙa'idojin Halal, da gina hanyoyin jigilar kayayyaki a yankuna daban-daban, tare da mayar da tattaunawar taron zuwa yarjejeniyoyin kasuwanci da ayyukan haɗin gwiwa.

A nata ɓangaren, Mataimakiyar Ministan Harkokin Wajen Vietnam, Nguyen Minh Hang, ta yaba da taken taron na bana wanda ya mayar da hankali kan ɗorewar ci gaba.

Ta ce tattalin arzikin Halal ya yi daidai da manufofin kare muhalli da samar da ci gaba mai ɗorewa.

Hang ta bayyana cewa tattalin arzikin Vietnam ya samu bunƙasar kashi 9 cikin ɗari a cikin watanni tara na farkon shekarar 2026.

Ta ce ƙasar na amfani da damar da take da ita a fannonin noma, da kamun kifi da sarrafa abinci, da kuma yarjejeniyoyin cinikayya cikin 'yanci guda 17 da ta ƙulla, domin gina ingantaccen tsarin tattalin arzikin Halal a cikin gida.

Ta ƙara da cewa Vietnam ta kafa Cibiyar Ba da Takardun Shaidar Halal ta Ƙasa, tare da fitar da dokar gwamnati kan kula da ingancin kayayyakin Halal, a ƙoƙarinta na samun gindin zama a cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya.

Yawon buɗe ido da ya dace da ƙasashen Musulmai

Hang ta bayyana muhimman fannoni uku da Vietnam ke son haɗin gwiwa da Turkiyya da sauran ƙasashen duniya a kansu.

Fannonin sun haɗa da ƙara kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashe, da ƙarfafa amincewa da takardun shaidar Halal na juna, da kuma bunƙasa fannin yawon buɗe ido da ya dace da al’ummar Musulmi tare da musayar ƙwararrun ma'aikata.

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Addini ta Turkiyya, Safi Arpagus, ya ce ya kamata a tabbatar da bin ƙa'idojin Halal a dukkan matakan samar da kayayyaki, maimakon mayar da hankali kan kayayyakin da aka gama sarrafa su kawai.

Ya yi gargaɗin cewa almubazzaranci wajen amfani da kayayyaki, lalata muhalli da kuma watsi da lafiyar ɗan Adam yayin samar da kayayyaki na haifar da babban barazana tare da cutar da al'ummomin da za su zo nan gaba.

Arpagus ya jaddada cewa gina aminci da masana'antar abinci ta Halal a duniya na buƙatar gaskiya, da kuma ɗaukar nauyi a kowane mataki na samar da kayayyaki.

Ya ce hakan na buƙatar tsarin bayar da takardun shaidar Halal da ƙwararrun masana kimiyya masu zaman kansu ke gudanarwa.

Ya kuma yi gargaɗin cewa bai kamata a bar aikin tabbatar da Halal a hannun mutanen da ba su da ƙwarewa ko waɗanda manufarsu ta kasuwanci ce kawai ba ce.

Ya yi alƙawarin ci gaba da aiki ƙarƙashin inuwar OIC domin ƙara wayar da kan jama'a da kuma ƙarfafa binciken kimiyya a fannin tattalin arzikin Halal.