Isra'ila ta yanke shawarar bude mashigar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar tare da ba da damar shigar da tallafin jinƙai zuwa Gaza, bayan ba ta gawarwakin mutane hudu da aka yi garkuwa da su a Gaza da aka yi, kamar yadda gidan kafar yaɗa labaran ƙasar Isra'ila, KAN ya ruwaito a ranar Laraba.
Isra'ila ta soke matakan da ta shirya ɗauka kan Hamas, wanda ya haɗa da rage yawan motocin tallafi da za su shiga yankin, in ji rahoton.
Tun da farko, an yanke shawarar rufe mashigar Rafah saboda Hamas ba ta miƙa gawarwakin fursunonin da take riƙe da su ba, ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, inda suka ce gano gawarwakin yana da wahala.
Isra'ila ta buƙaci a sauke kayan tallafi daga motocin a gefen iyakar Falasdinawa, inda daga nan kungiyoyin agaji da Majalisar Dinkin Duniya da ke Gaza za su karɓa.
“Muna bukatar dukkan mashigai su kasance a buɗe. Duk lokacin da mashigar Rafah ta kasance a rufe, hakan na wahalar da mutane a Gaza, musamman wadanda suka rasa matsugunansu a Kudu,” in ji mai magana da yawun UNICEF, Ricardo Pires.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza a ranar Litinin, yayin da aka yi musayar fursunonin Isra'ila da na Falasdinawa, waɗanda ya sa ake sa ran za a hanzarta kai kayan tallafi zuwa yankin, inda wani rahoton duniya kan yunwa ya gargadi cewa dubban mutane na fuskantar yunwa mai tsanani.
“Har yanzu muna ganin motocin tallafi kadan ne kawai ke shiga, kuma taron jama'a da ke zuwa wajen motocin yana da matukar wahala, ba ya bin ƙa'idojin jinƙai,” in ji mai magana da yawun ICRC, Christian Cardon, ga manema labarai a Geneva a ranar Talata.
Hukumar Abinci ta Duniya ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta ce a ranar Talata ta shigo da motocin tallafi 137 tun daga ƙarshen mako.
Ƙungiyoyin agaji na ƙoƙarin ƙara yawan kayan tallafi cikin gaggawa ga mutanen da ke birnin Gaza, inda mutum 400,000 ba su samu tallafi ba tsawon makonni, a cewar WFP.