| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Ƴan sandan Pakistan sun daƙile harin ƙunar baƙin wake da aka kai wa wasu ƴan Japan
Hukumomi a Pakistan sun daƙile wani mumunan hari da aka yi ƙoƙarin kai wa wasu ƴan ƙasar Japan a yayin da suke dab da tsallake harin kwanton ɓauna da wasu ƴan bindiga suka shirya musu.
Ƴan sandan Pakistan sun daƙile harin ƙunar baƙin wake da aka kai wa wasu ƴan Japan
  Wani mai magana da yawun yan sanda a Pakistan ya tabbatar da cewa wadanda suka tsira daga harin ƴan Japan ne kuma a halin da ake ciki suna karkashin kulawar jami'an. / Hoto: Reuters   / Others
19 Afrilu 2024

Ƴan sanda a birnin Karachi da ke yankin kudancin Pakistan sun harbe wani ɗan ƙunar baƙin wake da kuma wasu ƴan bindiga a lokacin da suke ƙoƙarin kai hari kan wata mota mai ɗauke da wasu ƴan kasar Japan biyar, waɗanda dukkansu suka tsira, a cewar mai magana da yawun ƴan sandan.

Ƴan bindigan waɗanda ke neman hamɓarar da gwamnati tare da kafa tsarin mulkinsu mai tsauri, sun ƙaddamar da wasu hare-hare mafi muni a Pakistan cikin ƴan shekarun da suka gabata, inda a wasu lokutan sukan kai hari kan ƴan kasashen waje, kamar ƴan China.

Waɗanda suka tsira daga harin ƴan Japan ne kuma a halin da ake ciki suna ƙarƙashin kulawar jami'an, a cewar mai magana da yawun ƴan sandan, Abrar Hussain Baloch, a ranar Juma’a.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

MAJIYA:TRT World