| hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Sojojin Turkiyya 20 sun yi shahada a hatsarin jirgin soji na dakon kaya a Georgia: Ma’aikatar Tsaro
Wani jirgin dakon kaya na Turkiyya ƙirar C-130 wanda ke kan hanyarsa daga Azerbaijan zuwa Turkiyya ya faɗi kusa da kan iyakar Azerbaijan da Georgia.
Sojojin Turkiyya 20 sun yi shahada a hatsarin jirgin soji na dakon kaya a Georgia: Ma’aikatar Tsaro
Ba gano silar hatsarin da adadin waɗanda suka rasu ba nan take
12 Nuwamba 2025

Ma’aikatar Tsaron Turkiya ta ce sojoji 20 sun yi shahada sakamakon hatsarin jirgin sama na dakon kaya na sojin Turkiyya a Georgia ranar Talata.

"Da misalin ƙarfe 06:30 na safiya (ƙarfe 02:30 agogon GMT) tare da haɗin gwiwar da hukumomin Georgia, aikin bincike da kuma tawagar masu bincike sun fara bincike kan tarkacen jirgin sojin na dakon kayan da ya faɗi a kan  iyakar Azerbaijan da Georgia," kamar yadda ma’aikatar ta bayyana ranar Laraba.

Wani jirgin dakon kayan soji na Turkiyya ƙirar C-130 ɗauke da jami’an soji 20 ya yi hatsari kusa da Azerbaijan a kan hanyarsa ta zuwa Turkiyya.

Masu AlakaTRT Afrika - Jirgin dakon kaya na sojin Turkiyya ya yi hatsari a iyakar Georgia-Azerbaijan dauke da jami'ai 20

Ma’aikatar ta kuma fitar da sunayen dukkan sojoji 20 da hatsarin ya kashe.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi tattaunawa ta waya ranar Talata da takwaransa na Azerbaijan Ilham Aliyev da kuma takwaransa na Georgia, Firaiminista Irakli Kobakhidze domin nazari kan abin da ya faru a baya bayan nan game da ayyukan bincike da ceto.

Da yake magana a wani taro a babban birnin ƙasar Ankara, Shugaba Erdogan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan sojojin da suka yi shahada.

Wasu ƙasashe da shugabanni daga sassan duniya sun miƙa saƙonninsu na jaje da ta’aziyya ga Turkiyya bayan hatsarin.

 

Rumbun Labarai
Turkish Airlines ya sayi hannun jari na dala miliyan 355 a kamfanin Air Europa na Spain
Erdogan ya yi Allah wadai da kashe fararen-hula a birnin Al Fasher na Sudan
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
Hamas ba ta da nukiliya, amma Isra'ila na da su: Erdogan ya nemi Berlin ta ɗauki mataki kan Tel Aviv
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Cikin hotuna: Yadda aka yi bukukuwa a duk faɗin kasa na cikar Ranar Jamhuriya ta Turkiyya ta 102
Turkiyya ta yi kira a tsagaita wuta nan-take a yaƙin da ake yi a birnin Al Fasher, Sudan
Turkiyya za ta mika wa dakarunta tankar yaki ta Altay da aka samar da yawa a karon farko
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Rumfar Karfe: Fasahar Turkiyya ta cikin gida mai aiki da Ƙirƙirarriyar Basira a sabon zamanin tsaro
Shugaba Erdogan ya shirya ziyartar yankin Gulf don haɓaka alaƙar tattalin arziki da ƙawance
Turkiyya ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar Afghanistan da Pakistan
An Fara Taron Yaki da Shara na ‘Zero Waste’ a Istanbul karkashin jagorancin Emine Erdogan
Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a bunkasa shigar mata cikin harkokin duniya
Cinikayya tsakanin Turkiyya da Afirka ta wuce $37b ana sa ran ta kai $40b a 2025: Minista
Turkiyya na da rawar da za ta taka a tsaron Turai, ta shirya domin aikin Gaza: Ministan Tsaro
Turkiyya ta yi maraba da amincewar majalisar dokokin TRCN kan ƙudurin samar da ƙasashe biyu
Ya kamata amincewar Ƙasashen Yamma da Falasɗinu ta zama silar samar da mafita ta ƙasa biyu: Erdogan