GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Kalaman Trump na lalata cibiyoyin nukiliyar Iran 'mafarki ne': Khamenei
Jagoran addinin na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ƙaryata kalaman Shugaban Amurka Donald Trump cewa hare-haren sama na Amurka sun lalata cibiyoyin nukiliyar Irana a watan Yuni.
Kalaman Trump na lalata cibiyoyin nukiliyar Iran 'mafarki ne': Khamenei
A watan Yunin 2025 ne Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran / AP
15 awanni baya

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei a ranar Litinin ya musanta iƙirarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa an lalata wuraren nukiliyar Iran ta hare-haren sama na Amurka a watan Yuni.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na intanet, Khamenei ya fada wa Trump cewa ya ci gaba da "mafarki" kan maganganun da ya yi game da lalatr wuraren, tare da tuhumar ikon Shugaban Amurka na "faɗa wa wata ƙasa abin da ya kamata ta mallaka ko kada ta mallaka idan tana da masana'antar nukiliya."

A tsakiyar watan Yuni, Isra'ila ta ƙaddamar da wani gagarumin hari ta sama kan Iran. Amurka ta shiga cikin wannan hari na dan lokaci, inda ta kai farmaki kan mahimman wuraren nukiliyar Iran.

A makon da ya gabata, yayin wani jawabi a majalisar Isra'ila, Trump ya sake nanata cewa Amurka ta tabbatar da "lalata" wuraren nukiliyar Iran yayin hare-haren.

Har yanzu ba a san tasirin hare-haren Amurka ba

"Mun jefa bama-bamai 14 a kan mahimman wuraren nukiliyar Iran. Kamar yadda na fada tun farko, mun lalata su gaba daya kuma an tabbatar da hakan," in ji Trump.

A wata hira da aka yi da shi a Fox News ranar Lahadi, Trump ya kuma ce “ a yanzu Iran ba ta tsoratar da yankin Gabas ta Tsakiya" bayan hare-haren Amurka da suka "lalata karfin nukiliyarta."

Ya kara da kiran hare-haren "aikin soja mafi kyau."

Har yanzu ba a san haƙiƙanin tasirin hare-haren da Amurkan ta kai ba.

Tattaunawar nukiliya ta tsaya cik

Ma'aikatar Tsaron Amurka ta ce hare-haren sun jinkirta shirin nukiliyar Iran da shekara daya zuwa biyu, wanda ya saɓa wa wani rahoton sirri na farko na Amurka da kafofin watsa labarai na Amurka suka bayyana cewa jinkirin ya kai watanni kadan kawai.

A ranar Litinin, Khamenei ya kira maganganun Trump "marasa dacewa, kuskure, da kuma nuna ƙarfi."

Yaƙin watan Yuni da Isra'ila ya faru ne kwanaki biyu kafin zagaye na shida na tattaunawar nukiliya da aka shirya tsakanin Tehran da Washington, wadda aka fara a watan Afrilu.

Tattaunawar nukiliya ta tsaya tun daga lokacin, inda Iran ta ce tana bude kofar tattaunawa ne kawai idan Amurka ta bayar da tabbacin cewa ba za ta sake ɗaukar matakin soja ba.