| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Adadin kuɗin da zakarun Gasar AFCON 2025 za su samu
Tawagar ƙasar da ta lashe kofin Ƙasashen Afrika na AFCON 2025 za su karɓi kyautar tsabar kuɗi dala miliyan $10, a yayin da tawaga ta biyu za samu dala miliyan $4, a cewar Hukumar CAF.
Adadin kuɗin da zakarun Gasar AFCON 2025 za su samu
Nijeriya suna da yakinin yin rawar gani a gasar AFCON ta 2025. / Reuters
21 awanni baya

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta ƙara yawan kuɗaɗen da za ta raba wa zakarun gasar kofin ƙwallon ƙafa na Afirka ta AFCON 2025.

Tawagar ƙasar da ta lashe kofin za ta samu ladan kuɗi dala miliyan $10, yayin da ƙungiyar da ta sha kaye a wasan ƙarshe za ta karɓi dala miliyan $4,000,000.

Tun gabanin fara gasar da aka ƙaddamar Lahadin da ta gabata 21 ga Disamba ne shugaban hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe ya bayyana wannan ƙarin da aka samu.

Wannan babban ƙari ne idan aka kwatanta da na 2023, lokacin da zakarun wancan shekara, Ivory Coast suka samu dala miliyan $7, kuma ƙasa ta biyu, Nijeriya, ta samu ladan dala miliyan $4.

A gasar da ke gudana a Maroko, ƙungiyoyin da suka fice a matakin dab da na ƙarshe za su samu aƙalla dala miliyan $2.5 kowacce, yayin da waɗanda suka kai wasan kusa da na ƙarshe za su karɓi aƙalla dala miliyan $1.3.

Ƙungiyoyin da aka fitar daga gasa a zagayen ‘yan-16 za su samu dala dubu $800 kowacce.

Jimillar kuɗin lada

Ƙungiyar da ta taka rawar gani amma ta zo ta uku a matakan rukuni, za ta samu dala dubu $700, yayin da ƙasashen da suka fice daga gasa a matakin rukuni za su samu dala dubu $500 kowacce.

Baya ga ladan da za a bai wa zakaru, wanda aka ƙara da kashi 43%, sauran ƙungiyoyin za su samu kuɗaɗe kusan daidai da na waɗanda suka fita daga gasar a 2023 a irin waɗannan matakai.

Ƙungiyoyi 24 ne ke halartar AFCON a wannan shekara, kuma jimillar kuɗn ladan da aka ware musu su duka shi ne dala miliyan $32.