Ghana ta tura injiniyoyin soji 54 zuwa Jamaica domin taimaka wajen sake gina ababen more rayuwa bayan mahaukaciyar guguwa mai suna Hurricane Melissa ta kashe sama da mutum 40 kuma ta lalata ababen da kimasu ta kai dala biliyan $8.8, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ta bayyana ranar Laraba.
Dakarun rundunar injiniyoyi ta 14 na rundunar sojin ƙasar Ghana za ta ba da tallafi na aikin injiniya da sake gini da jigila yayin da Jamaica ke ƙoƙarin sake dawo da al’ummomin da lamarin ya shafa tare da abokanan aiki na ƙasa da ƙasa, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a shafinsa na Facebook.
Shugaba John Dramani Mahama da manyan jami’an gwamnati da kwamandojin soji da jami’an diflomasiyya da wakilan Jamaica sun halarci bikin tafiyarsu.
Mahama ya ce tura sojojin ya nuna goyon bayan Ghana ga Jamaica da kuma yanayi na jinƙai da fasaha na aikin, yana mai bayyana sojojin a matsayin jakadun da aka ɗaura wa nauyin aikin ijniyi da sake gini da tallafa wa al’umma.
Hadin kan Afirka da Caribbean
Ya sake tabbatar da jajircewar Ghana kan haɗin kan Afirka da Caribbean da kuma haɗin kan ƙasashen kudancin duniya.
Ministan harkokin wajen ƙasar Samuel Okudzeto Ablakwa ya bayyana cewa manufar harkokin waje na ƙasar Ghana na aiki ne "bisa jajircewa kan hadin kai da kuma tallafi ga ƙasashen da ke buƙata " kuma ya ambato tallafin jinƙai da ta bai wa Falasdinu da Cuba da kuma Sudan.
Ya bayyana cewa an tura sojojin ne bisa buƙatar da Firaymin Ministan Jamaica Andrew Holness ya gabatar a hukumance .
Mace-mace da ta’adi mai yawa
Mahaukaciyar guguwar Hurricane Melissa ta afka wa ƙasashen Haiti da Jamaica da Cuba a ƙarshen watan Oktoba, inda ta janyo lalace ababuwa da rasa rayuka.
Adadin waɗanda suka mutu a Haiti da Jamaica daga ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa da guguwar ta jnayo ya kai 88 zuwa ranar 2 ga watan Disamba, ciki har da aƙalla mutum 45 a Jamaica da kuma mutum 43 a Haiti, in ji cibiyar ba da agaji ga waɗanda bala’i ya sama.















