Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya sanar da dakatar da bayar da biza ga ‘yan Nijeriya daga ranar 1 ga Janairun 2026.
Rahotanni sun ce wannan mataki ya biyo bayan sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar da ke cewa daga karfe 12.01 na daren ranar 1 ga Janairun 2026, za su dakatar da bayar da biza ga wasu daga cikin ‘yan ƙasashen waje 19 da suka haɗa da Nijeriya, Angola, Cuba, Venezuela da wasu ƙasashe da dama.
A wani saƙo da Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar ta shafinsa na X ranar Litinin da daddare ya bayyana nau’ukan bizar da Amurka za ta daina bai wa ‘yan Nijeriya.

“Daga karfe 12.01 na daren ranar 1 ga Janairun 2026, sakamakon Matakin da Shugaban Ƙasa ya ɗauka mai lamba 10998 kan “Hanawa da Taƙaita Shigar ‘Yan Ƙasashen Waje don Kare Tsaron Amurka,” Ma’aikatar Harkokin Waje ta dakatar da bayar da biza nau’in B-1/B-2 da ba ta ‘yan gudun hijira ba, da F, M, J na ɗalibai da musayar maziyarta, da ma dukkan nau’ukan bizar masu gudun hijira ga ‘yan ƙasashen duniya 19 da suka haɗa da: Angola, Antigua and Barbuda, Benin, Burundi, Cote D’Ivoire, Cuba, Dominica, Gabon, The Gambia, Malawi, Mauritania, Nijeriya, Senegal, Tanzania, Togo, Tonga, Venezuela, Zambia, da Zimbabwe,” in ji sanarwar.
Sai dai matakin na shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da togaciya ga wani rukunin mutane daga wasu ƙasashe da suka haɗa da ‘yan tsiraru ta fuskar addini da ƙabila na ƙasar Iran da za a dinga bai wa bizar ‘yan gudun hijira.
Kazalika matakin bai shafi masu ɗauke da fasfon wata ƙasa da za su nemi biza da fasfon ƙasarsu ta biyu da ba ta jerin ƙasashen da matakin ya shafa.
Sannan an bayyana lamarin bai shafi bizar baƙi ta musamman ga ma’aikatan Amurka ƙarƙashin tsarin 8 U.S.C. 1101(a)(27)(D), da kuma mahalarta bukukuwan wasanni, da kuma mazauna na dindindin da ke bisa ƙa’ida.

















